An tsinci jarirai 18 da ransu cikin wata 4 kacal a garin Funtua

An tsinci jarirai 18 da ransu cikin wata 4 kacal a garin Funtua

- Shugaban hukumar bada ilimi da samar da walwalar jama’a na jihar Katsina Ibrahim Nasir yace an tsinto jarirai 18 cikin wata 4 a garin Funtua.

- Yace akan tsinto jariranne a makwararrun ruwa, Juji, kwata da gidajen da ba’a gama gininsu ba.

An tsinci jarirai 18 da ransu cikin wata 4 kacal a garin Funtua

An tsinci jarirai 18 da ransu cikin wata 4 kacal a garin Funtua

Ibrahim Nasiru yace abin ya zama ruwan dare a yankin domin ko a jiya 24 ga watan Janairu an tsinto wata jaririya a wata tsohuwar masai.

Yace abin fa yanzu ya zama ruwan dare a gari na Funtua.

A wani labarin kuma daga jihar ta Katsina, Habiba Ishaku 'yar kimanin shekara 18 da haihuwa ta kalubalanci iyayenta a gaban kuliya manta sabo, a jihar Katsina.

KU KARANTA KUMA: Iya kudin ka-iya shagalin ka! Sarkin Kano yayi watsi da dokar auren Danbatta

Habiba wadda asalinta ba musulma ba ce ta shigo Musulunci ne a shekarar da ta gabata, inda ta auri wani matashi mai suna Jamilu Lawan ba tare da amincewar mahaifanta ba.

A zaman kotun da aka yi tsakanin Habiba da mahaifanta karkashin jagorancin kungiyar kiristoci mabiya majami'ar ECWA, iyayen nata sun kalubalanci komawar ta Musulunci, a inda suka ce Habiba yarinya ce karama kuma shekarunta 14 ba 18 ba kamar yadda ta ce, in ji mahaifinta Mr. Ishaku Tanko.

Habiba 'yar asalin karamar hukumar Kankara dake jihar Katsina ta gabatarwa mai shari'a Baraka Isiyaku Wali takardar haihuwarta da ta nuna shekarun ta 18.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda

Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda

Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel