Rashawa: An bukaci Buhari ya rika sara yana duban bakin gatari

Rashawa: An bukaci Buhari ya rika sara yana duban bakin gatari

Kungiyar da ke yaki da rashawa Transparency Internationalta fitar da rahotonta na shekara game da matsayin rashawa a kasashen duniya. Kungiyar ta yi amfani da alkalumman Bankin duniya da kuma Bankin raya kasashen Afirka a bincikenta kafin fitar da rahoton.

Rashawa: An bukaci Buhari ya rika sara yana duban bakin gatari

Rashawa: An bukaci Buhari ya rika sara yana duban bakin gatari

Bankin Duniya da kuma bankin raya kasashen Afirka ADB na a matsayin madogara da Transparency International ta yi amfani domin jera sunayen kasashen duniya a game da yadda ake karbar rashawa a sassan duniya.

Kasashen New Zealand da Danemark da Finland da kuma Sweden ne a matsayin wadanda suka fi taka rawa wajen rage karfin rashawa a tsakanin al’umma inda suka samu maki da ya kama daga 90 zuwa 80 cikin dari.

Kasashen Jamus da Luxembourg da Birtaniya da kuma Amurka, na cikin kasashen da ke sahu na biyu da makin da ya kama daga 80 zuwa 69 cikin dari a ma’aunin Transparency International.

KU KARANTA KUMA: Wankewar da Buhari yayi ma Babachir na ci gaba da tada kura (Karanta)

Sai dai kungiyar mai yaki da rashawa ta bayyana cewa har yanzu wannan matsala na ci gaba da kasancewa a matsayin kadangaren bakin tulu musamman a kasashen masu tasowa.

Libya da Sudan da Sudan ta Kudu da kuma Somalia, na matsayin kasashen da ke can sahun karshe da matsalar ta yin kamari, kuma ga alama babu alamar samun inganci a kasashen lura da rahoton da ya gabata a shekarar bara.

Rahoton ya ce matsalar ta karu a kasashe da dama a shekarar da ta gabata, tare da yin kiran kara daukar matakan yaki da matsalar rashawa a duniya.

Rahoton ya kuma yi kira ga shugabannin kasashen Afrika da suka lashe zabe da niyyar yaki da rashawa kamar Najeriya da su yi kokarin cika alkawalin da suka dauka ga ‘Yan kasa amma ta hanyar bin tsarin dokokin kasa da kaucewa take hakkin dan adam.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel