Tinubu ya kara jaddada goyon bayan sa ga Buhari

Tinubu ya kara jaddada goyon bayan sa ga Buhari

- Tsohon gwamnan jihar Legas kuma jigo jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu y ace shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi abin da tsohon Shugaban Goodluck Jonathan ya kasa yi a tsawon mulkinsa.

- Tinubu ya fadi hakanne a jawabinsa a Kwalejin Tsaro da ke Abuja.

Tinubu ya kara jaddada goyon bayan sa ga Buhari

Tinubu ya kara jaddada goyon bayan sa ga Buhari

Tinubu ya jinjina ma sojojin Najeriya akan nasarorin da ta samu a yaki da Boko Haram.

Bayan haka kuma ya kara jinjin ma shugaban kasa akan rashin takura ma gidajen jaridu da gwamnatinsa ba sayi da kuma walwala da aka samu a harkar.

KU KARANTA KUMA: Najeriya ta kusa bankwana da dauke wuta - Fashola

Daga karshe y ace jam’iyyar sa ta APC za ta cigaba da samar da ingantattun ayyuka domin mutanen Najeriya kamar yadda tayi alkawari.

Awani labarin kuma, Wani tsohon ministan kwadigo Joel Ikenga kuma jigo a jam’iyyar PDP ya canza sheka daga jam’iyar zuwa jam’iyar APC.

Joel ya sanar da hakanne da yake ganawa da manema labarai ranar Litini a jihar Taraba.

Ya yi bayanin cewa dalilin sauya shekar nasa shine domin ganin irin nasarori da kyawawan ayyuka da wannan gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta ke ta aiwatarwa tun daga lokacin da ta hau karagar mulki.

Bayan haka kuma ya ce ya gamsu da yaki da cin hanci da rashawa da wannan gwamnati ta sa a gaba.

Tsohon minista Joel ya kara da cewa cikin dalilan da ya sa ya fice daga jam’iyyar PDP shine domin nasarorin da aka samu wajen yaki da kungiyar Boko Haram da kokarin dawo da zaman lafiya a yakin arewa maso Gabas.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Za’a sake ɗiban wasu sabbin hafsoshin rundunar Yansanda – Gwamnatin tarayya

Za’a sake ɗiban wasu sabbin hafsoshin rundunar Yansanda – Gwamnatin tarayya

Canji! Gwamnatin shugaba Buhari zata sake ɗiban sabbin hafsoshin Yansanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel