Sunyi ma yara fyade sannan suka basu ladar N100 a Kano

Sunyi ma yara fyade sannan suka basu ladar N100 a Kano

Wata kotu a jihar Kano ta gurfanar da wadansu magidanta masu suna Babangida Ubale da Isyaku Musa ‘yan asalin karamar hukumar Bichi da laifin aikata fyade akan wadansu kananan ‘yan mata masu talla.

Sunyi ma yara fyade sannan suka basu ladar N100 a Kano

Sunyi ma yara fyade sannan suka basu ladar N100 a Kano

Kamar yadda mai shigar da kara ya fadi, Babangida da isiyaku sun rudi ‘yan matanne cewa za su siya kayansu sai suka kule da su wani gida suka cire musu kamfai kuma sukayi musu fyade.

Babangida da Isiyaku sun ba yaran kyautar naira 100 bayan sun gama.

A wani labarin kuma, Habiba Ishaku 'yar kimanin shekara 18 da haihuwa ta kalubalanci iyayenta a gaban kuliya manta sabo, a jihar Katsina.

KU KARANTA KUMA: Yan kato-da-gora sun kama yan Boko Haram 3 a jihar Zamfara

Habiba wadda asalinta ba musulma ba ce ta shigo Musulunci ne a shekarar da ta gabata, inda ta auri wani matashi mai suna Jamilu Lawan ba tare da amincewar mahaifanta ba.

A zaman kotun da aka yi tsakanin Habiba da mahaifanta karkashin jagorancin kungiyar kiristoci mabiya majami'ar ECWA, iyayen nata sun kalubalanci komawar ta Musulunci, a inda suka ce Habiba yarinya ce karama kuma shekarunta 14 ba 18 ba kamar yadda ta ce, in ji mahaifinta Mr. Ishaku Tanko.

Habiba 'yar asalin karamar hukumar Kankara dake jihar Katsina ta gabatarwa mai shari'a Baraka Isiyaku Wali takardar haihuwarta da ta nuna shekarun ta 18.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sanata Shehu Sani ya lissafa wasu muhimman matakai daya zama wajibi a ɗauka don sake raya Arewa

Sanata Shehu Sani ya lissafa wasu muhimman matakai daya zama wajibi a ɗauka don sake raya Arewa

Farfaɗo da martabar Arewa: Muhimman matakai guda 10 da ya dace yan Arewa su ɗauka – Shehu Sani
NAIJ.com
Mailfire view pixel