Yan adawan Buhari ne rura wutar rikicin kudancin Kaduna

Yan adawan Buhari ne rura wutar rikicin kudancin Kaduna

Kungiyar yan siyasan addinin kirista na yankin Arewacin Najeriya (The Northern Nigeria Christian Politicians -NNCP) ta bayyana cewar masu ingiza kashe kashen da ake yi a kudancin Kaduna yaran wasu abokan hamayyar shugaba Buhari ne, wadanda suka dauki alwashin ruguza gwamnatin nasa.

Yan adawan Buhari ne rura wutar rikicin kudancin Kaduna

Shugaban kungiyar Keftin Amuga ne ya shaida ma manema labarai haka a birnin Abuja, inda yayi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da yarda da wannan nufi nasu, saboda abinda suka sanya a gaba shine kudi.

KU KARANTA:Halin matsin tattalin arziki: Gwamnatin tarayya zata ƙara ma ma’aikata albashi

Amuga ya jaddada cewar babu rowan Fulani a cikin kai hare haren da ake yi, inda yace yaushe ma Fulani mai sanda zai iya kai wannan hari, don haka Amuga ya bukaci shugaba Buhari da kada ya sassauta ma duk wanda aka kama da laifi, idan bah aka ba ba zasu taba yarda kokarinsa na samar da zaman lafiya a yanki ya ci nasara ba.

“Kungiyar mu ta NNCP na jimamin rikicin dake faruwa a yankin Kudancin Kaduna da makwabtan jihohin Nasarawa, Binuwe, Filato da Taraba, kuma mun yi tir das hi. Don haka muke kira ga gwamnati data hukunta duk wanda aka kama da hannu a ciki, tun daga masu daukan nauyi, zuwa masu zartarwa,” inji Amuga.

Amuga ya shawarci gwamnoni, Sarakuna, shuwagabannin addininai dana siyasar Arewa dasu fada ma kawuanansu gaskiya, su fitar da masu rura wannan rikicin, sa’annan su hada kai da shugaban kasa wajen gano bakin zaren, don samar da cigaba dawwamamme a yankin.

Daga karshe Amuga ya yaba ma matakin da shugaba Buhari ya dauka na yin watsi da bukatar majalisar dattawa da tace lallai sai ya kori sakataren gwamnati Babachir David Lawal, inda yace, “yin hakan cin karo ga dokar bin tsari wajen gudanar da ayyukan gwamnati, ko da an ta yi ma shugaban bita da kulli kenan”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel