Gwamna Ganduje ya kaddamar da ginin katafaren shagun zamani a jihar Kano

Gwamna Ganduje ya kaddamar da ginin katafaren shagun zamani a jihar Kano

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya shaida ma kanawa a ranar Alhamis cewar ba zai taɓa satan kudaden al’umma ba, ko ya karkatar dasu.

Gwamna Ganduje ya kaddamar da gini katafaren shagun zamani a jihar Kano

Gwamna Ganduje

Ganduje ya bayyana haka ne yayin dayake sanya fandisho na kaddamar da ginin katafaren rukunin shagunan zamani mai dauke da shaguna 4,128 na masu sana’ar siyar da atamfofi dake kasuwar Kwari.

Ana sa ran ginin zai lashe kimanin kudi naira biliyan 5, amma gwamna Ganduje yace kimanin naira miliyan 917 daga cikin kudin za’a kashe su ne wajen gina hanyoyin da suka nufi kasuwar.

KU KARANTA:Musulmai a kasar Amurka sun gudanar da gangamin rashin amince da wani shirin shugaba Donald Trump

Sa’annan ya kara da cewa za’a gina wasu sabbin shaguna 336 akan kudi naira miliyan 801, inda kuma za’a sake gina wasu shagunan da yawansu ya kai 280, su kuma akan kudi naira miliyan 667.

Gwamna Ganduje yayi alkawari gwamnatinsa zata sabunta fuskokin kasuwannin Kurmi, Kwari, Yan Lemo da Dawanau.

A nasa barayin, San Kano Alhaji Muhammadu Sunusi II ya gargadi kanawa da su cigaba da taimaka ma jami’an tsaro wajen magance miyagun laifuka, daga karshe yayi kira ga yan kasuwa su tabbatar da suna fitar da Zakkah daga dukiyoyinsu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile faruwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile faruwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile afkuwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma
NAIJ.com
Mailfire view pixel