Abin da ya hana Shugaba Buhari magana daga Landan

Abin da ya hana Shugaba Buhari magana daga Landan

– Fadar Shugaban Kasa ta bayyana dalilin da ya hana Shugaba Buhari magana daga Landan

– Mai ba Shugaban Kasa shawara kan harkokin yada labarai yace Shugaba Buhari hutu ya tafi ba Asibiti ba

– Fadar Shugaban Kasa ta kara karyata rade-radin da ke ta yawo

Abin da ya hana Shugaba Buhari magana daga Landan

Abin da ya hana Shugaba Buhari magana daga Landan

Fadar Shugaban Kasa ta bayyana cewa hutu ya kai Shugaba Buhari Landan ba ganin Likita ba. Femi Adesina; mai ba Shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai yace yanzu haka Shugaba Buhari ba ya wani Asibiti.

Mai ba Shugaban kasar shawara kan harkokin yada labarai, Femi Adesina ya bayyana dalilin da ya hana Shugaba Buhari yayi magana daga Landan inda yake. Adesina ya bayyana wa gidan talabiji CNBC Africa cewa za a matsawa Shugaban Kasar idan har aka ce sai yayi magana daga inda yake hutun sa.

KU KARANTA: Ni ban ce Buhari ya mutu ba-Saraki

Femi Adesina dai ya tabbatar da hirar da yayi da gidan jaridar cewa Shugaban Kasar na cikin koshin lafiya sabanin yadda jita-jita ke yawo a gari. Femi Adesina a baya ya bayyana cewa Shugaba Buhari bai taba rashin lafiya a Fadar Aso Rock ba.

Ana ta yada rade-radin cewa Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo na shirin ajiye aiki bayan matsin lamba da yake samu daga wasu Gwamnoni. Haka Fadar Shugaban Kasa dai ta yi wuf ta maida martani ga masu yada jita-jitar inda tace sam karyar banza ce ba gaskiya ba.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Za’a sake ɗiban wasu sabbin hafsoshin rundunar Yansanda – Gwamnatin tarayya

Za’a sake ɗiban wasu sabbin hafsoshin rundunar Yansanda – Gwamnatin tarayya

Canji! Gwamnatin shugaba Buhari zata sake ɗiban sabbin hafsoshin Yansanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel