Kasassaɓarsa: kotun Amurka na neman Sanata Buruji Kashamu ruwa a jallo

Kasassaɓarsa: kotun Amurka na neman Sanata Buruji Kashamu ruwa a jallo

Wata kotun daukaka kara ta kasar Amurka ta yanke hukuncin jami’an tsaron Amurka nada damar kama wani Sanata dan Najeriya, Sanata Buruji Kashamu a duk inda yake, inda tace don haka ya zama wajibi a cafko mata shi.

Kasassaɓarsa: kotun Amurka na neman Sanata Buruji Kashamu ruwa a jallo

Sanata Buruji Kashamu

Jaridar Washington Post ta ruwaito kotun ta yanke hukuncin ne bayan watsi da tayi da karar da shi Sanata Kashamu ya shigar a gabanta a matsayin daukaka kara, don ta hana hukumomin tsaro kamo shi don fuskantar zarge zargen dake kansa na safarar kwayoyi zuwa kasar Amurka.

KU KARANTA:Musulmai a kasar Amurka sun gudanar da gangamin rashin amince da wani shirin shugaba Donald Trump

Ana zargin Kashamu wanda a yanzu Sanata ne mai wakiltar al’ummar Ogun ta tsakiya ne da kasancewa jagoran wasu kungiyoyi da suka shahara wajen siyarwa tare da safarar kwayoyi a garin Chicago na kasar Amurka kimanin shekaru 30 da suka gabata.

A watan Afrilun 2015 ne dai Sanata Kashamu ya roki kotun Allah da Annabi data dakatar da umarnin kamo shi da wata babbar kotun kasar Amurka ta bayar. Sai dai yayin da Alkalin kotun daukaka karar yake yanke hukuncin, yayi watsi da bukatar Kashamu, inda yace hukuncin babbar kotun yayi daidai da doka.

A cewar Alkalin kotun, ba za’a kira umarnin kamo Kashamu da sunan ‘sato shi’ ba.

Sai dai Sanata Kashamu yayi ikirarin cewar kage kawai ake yi mai, inda yace hukumomin kasar Amurka suna neman kaninsa ne ba shi ba, amma a cewarsa sun kasa ganewa.

Duk da cewa wadanda aka kama da dama da hannun a cikin aikata mummunar laifin sun amsa laifinsu, amma Kashamu yace atafau ba shi ake nema ba, kuma bai ga yadda za ayi ya amsa laifin kaninsa ba, wanda ya riga ya mutu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile faruwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile faruwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile afkuwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma
NAIJ.com
Mailfire view pixel