‘Yan Bindiga sun sace Sarkin Hausawa

‘Yan Bindiga sun sace Sarkin Hausawa

– ‘Yan Bindiga sun sace wani Sarkin Hausawa a Jihar Kogi

– An dai sace Sarkin ne yayin da yake ta sharar bacci

– Jama’a sun shiga cikin rudu a Yankin

‘Yan Bindiga sun sace Sarkin Hausawa

‘Yan Bindiga sun sace Sarkin Hausawa

Tsagerun mutanen Agatu sun sace wani Sarki na Hausawa a Jihar Kogi yayin da ya ke ta sharar bacci cikin dare. Wannan abu dai ya faru ne a yankin Bagana da ke cikin karamar hukumar Omala a Jihar Borno.

‘Yan Bindigan Agatu daga jihar Benuwe ne suka sace wannan Sarki Alhaji Audi Musa, bayan da suka afkawa Garin Bagana a farkon wannan makon. Wannan abu dai ya sa Jama’ar garin sun shiga cikin wani hali, da dama dai sun fara tserewa daga Garin.

KU KARANTA: Mutane 2 sun hallaka a yayin rikicin kungiyoyin matasa a jihar Kaduna

Bayanai sun nuna cewa kusan ‘Yan bindiga 20 suka kutso kai cikin Garin, inda suka yi gaba da Sarkin cikin dare. ‘Yan Bindigan sun shigo ne da manyan makamai wanda suka shiga harbawa a saman iska domin ba Jama’a tsoro. Hukumar ‘Yan Sanda ta tabbatar da hakan, sai dai tace za ta kamo ‘Yan bindigan.

Kamar yadda muka kawo rahotanni a baya. Wasu daga cikin ‘Yan Kungiyar IMN ta Shi’a sun gwabza da Jami’an tsaro na ‘Yan Sanda a Garin Abuja inda ‘Yan Kungiyar ke zan-zanga nema a saki Malamin su, Ibrahim Zakzaky, da dama dai sun samu rauni a karawar.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim
NAIJ.com
Mailfire view pixel