Mutane 2 sun hallaka a yayin rikicin kungiyoyin matasa a jihar Kaduna

Mutane 2 sun hallaka a yayin rikicin kungiyoyin matasa a jihar Kaduna

Mutane biyu ne aka ruwaito sun sheka lahira sakamakon wata takaddama data kaure tsakanin matasan Unguwar Shanu da na Unguwar Sarki, dake makwabtaka da juna a cikin birnin jihar Kaduna.

Mutane 2 sun hallaka a yayin rikicin kungiyoyin matasa a jihar Kaduna

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewar an somo rikicin ne a lokacin da matasan Unguwar Shanu ne suka kai wani hari wanda ake kira da suna ‘shara’ a yankin Unguwar Sarki da misalin karfe 9 na daren Litinin.

Sai dai hausawa na cewa ‘kaikayi koma kan mashekiya’ sai ga shi an jikkata matasan unguwar shanun har su hudu, da suka hada da Tasiu Abdulahi, Yusuf Garba, Abdulahi Sani da Nasiru Lawal.

KU KARANTA: Yan Najeriya sun yi jimamin mutuwar wata jarumar Soja mace

Sarkin Unguwar Shanu, Malam Aliyu Gumi ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace a yanzu haka sun rigaya sun binne Tasiu Abdullahi da Yusuf Garba, mutum biyu da suka rasa rayukansu yayin fadan.

Sarki Aliyu Gumi yace “labarin daya zo mana shine, matasan Unguwar shanu ne suka kai farmaki Unguwar Sarki, inda aka kashe mutane biyu, sa’annan aka jikkata mutane biyu, wanda a yanzu haka daya na hannun yansanda, daya kuma na asibitin Barau Dikko.”

Yayin da muka tuntubi hukumar yansanda, Kaakakin hukumar ASP Aliyu Usman ya tabbatar da faruwar lamarin, kuma yace suna cigaba da gudanar da bincike.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Za’a sake ɗiban wasu sabbin hafsoshin rundunar Yansanda – Gwamnatin tarayya

Za’a sake ɗiban wasu sabbin hafsoshin rundunar Yansanda – Gwamnatin tarayya

Canji! Gwamnatin shugaba Buhari zata sake ɗiban sabbin hafsoshin Yansanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel