Oyegun na shirin korar su Tinubu daga APC

Oyegun na shirin korar su Tinubu daga APC

– Kwamared Timi Frank ya bayyana cewa Shugaban APC, Cif Oyegun na shirin korar wasu manyan Jam’iyyar

– Timi Frank ya zargi Oyegun da saba dokar Jam’iyya sau da yawa

– Frank yace Oyegun na shirin korar irin su Atiku da Bola Tinubu daga Jam’iyyar

Oyegun na shirin korar su Tinubu daga APC

Oyegun na shirin korar su Tinubu daga APC

Kwamared Timi Frank, wanda shine Mataimakin mai magana da bakin Jam’iyyar APC ya bayyana cewa Shugaban Jam’iyyar Cif John Oyegun na shirin korar wasu manyan ‘yan Jam’iyyar irin su Atiku Abubakar da Bola Ahmed Tinubu.

Frank ya bayyana wannan ne a wani jawabi da ya rubuta ya kuma rattaba hannun sa, ya mikawa manema labarai a Jiya. Frank yace Oyegun na kokarin korar duk wadanda su kayi maganar da ba tayi masa dadi ba.

KU KARANTA: Gwamna Abu Lolo yayi magana

Timi Frank ya zargi Cif Oyegun da saba dokar da ta kafa Jam’iyyar ba sau daya ba-ba sau biyu ba. Kwanan nan APC din za tayi babban taron ta, sai dai Timi Frank din yace akwai lauje cikin nadi a wannan taro da za ayi.

Kwanakin bayan nan ne Bola Ahmed Tinubu ya bayyana dabarun siyasar da suka yi har suka naka PDP da Kasa war-was a zaben 2015. Bola Tinubu yayi wannan bayani ne yayin da ya ke gabatar da takarda game da rayuwar siyasar sa a Kwalejin Soji da ke Abuja a Jiya.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile faruwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile faruwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile afkuwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma
NAIJ.com
Mailfire view pixel