Me yayi zafi: Ta kashe kan ta saboda MMM

Me yayi zafi: Ta kashe kan ta saboda MMM

– Wata mata ta kashe kan ta a dalilin tsarin nan na MMM

– Wannan mata dai tana da ‘ya ‘ya har biyu

– Wannan abu ya faru ne a Garin Makurdi na Jihar Benue

Me yayi zafi: Ta kashe kan ta saboda MMM

Me yayi zafi: Ta kashe kan ta saboda MMM

MMM dai yayi sanadiyar mutuwar wata mata mai shekaru 34 a Garin Makurdi da ke cikin Jihar Benue. Wannan mata dai mai suna Gloria Samson tana da ‘Ya ‘ya har biyu.

Abun dai da ya faru shine wannan mata ta ci wasu tarin bashi har wurare hudu, bayan nan kuwa ta zuba wannan kudi a cikin tsarin nan na MMM tana mai sa ran ta ja kaya, ko da tayi haka kenan sai aka rufe tsarin a karshen wancan shekarar. Shi ke nan fa aka sha ta misilla!

KU KARANTA: Saurayi ya sadaukar da rayuwar sa domin wasu su rayu

Wannan mata dai ta bar gida a karshen Disamba ta jefa kan ta cikin rafi, sai dai gawar ta ‘Yan Sanda suka gani bayan ‘yan kwanaki. Wannan mata dai sai da ta nemi gafarar ‘ya ‘yan ta biyu kafin ta jefa kan ta cikin rafin. Marigayiyar dai ta ci bashin banki har kimanin N400, 000 ta jefa cikin MMM.

Kwanaki Babban Faston Cocin Omega Fire Ministry International yayi kaca-kaca da tsarin nan na MMM. Babban Faston ya kira mabiyan sa da su guji shiga irin wannan tsari, Faston yace MMM din Haramun ne. Mutane da dama dai sun shiga cikin wannan tsari na MMM tsindum.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu

Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu

Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu
NAIJ.com
Mailfire view pixel