Juyin mulki: Hukumar CIA ta san abin da zai faru a 1985

Juyin mulki: Hukumar CIA ta san abin da zai faru a 1985

– Ashe Kasar Amurka tana da labarin za a kifar da gwamnatin Buhari a 1985

– Babangida 'IBB' ya kifar da Gwamnatin Buhari a wani juyin mulki

– Ashe CIA ta Amurka ta san duk abin da zai faru

Hukumar CIA ta san abin da zai faru a 1985

Hukumar CIA ta san abin da zai faru a 1985

Wasu bayanan sirri da muke samu daga Hukumar bincike ta Amurka watau CIA sun nuna cewa ashe Kasar Amurka tana da masaniyar cewa za a hambarar da Gwamnatin Janar Buhari shekaru 30 da suka wuce.

CIA tana da labarin wanda zai kifar da Gwamnatin Janar Buhari da kuma lokacin da za a yi wannan juyin mulki. CIA ta gano cewa za a yi wa Buhari juyin mulki a shekarar 1985 lokacin da tattalin arzikin Kasar da kuma goyon bayan wasu ya fara tabarbarewa.

KU KARANTA: Donald Trump ya fara koro bakaken fata daga Amurka

An dai samu rashin jituwa a tsakanin Sojojin Kasar musamman kanana da suka fito daga Kudancin Kasar lokacin Janar Buhari yana mulkin Soji. Tun lokacin dai CIA tace ba za a dade ba, za a kifar da Gwamnatin sa.

A jiya kuma Fadar Shugaban Kasa ta bayyana cewa hutu ya kai Shugaba Buhari Landan ba ganin Likita ba. Femi Adesina; Mai ba Shugaban Kasa shawara kan harkokin yada labarai yace yanzu haka Shugaba Buhari ba ya wani Asibiti.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Buhari ya amince a sayo jiragen ruwa don toshe kafofin barna da samar da tsaro a hanyoyin ruwa

Buhari ya amince a sayo jiragen ruwa don toshe kafofin barna da samar da tsaro a hanyoyin ruwa

Buhari ya amince a sayo jiragen ruwa don toshe kafofin barna da samar da tsaro a hanyoyin ruwa
NAIJ.com
Mailfire view pixel