Kungiyoyin kasashen duniya sun jinjina ma Buhari kan yaki da cin hanci da rashawa

Kungiyoyin kasashen duniya sun jinjina ma Buhari kan yaki da cin hanci da rashawa

Jadawalin rabe raben kasashen duniya da matsayinsu dangane da mu’amala da rashawa wanda wata kungiya mai zaman kanta ta Duniya wato ‘Transparency Internationational ta gudanar ya bayyana kasar Najeriya a matsayin guda cikin kasashen da suka rungumi yaki da cin hanci da rashawa bil haqqi.

Kungiyoyin kasashen duniya sun jinjina ma Buhari kan yaki da cin hanci da rashawa

Shi dai wannan jadawalin ya kunshi kasashe 176 ne, inda ya farad a lissafa kasashen dake da karancin matsalar cin hanci da rashawa zuwa kasashen da suka cirri tuta a fagen aikata cin hanci da rashawa.

KU KARANTA: Halin matsin tattalin arziki: Gwamnatin tarayya zata ƙara ma ma’aikata albashi

Sai dai a wannan karo, matsayin Najeriya a jadawalin yayi sama, wanda ke nuna cewar an samu ci gaba a yakin da ake yi da cin hanci da rashawa a kasar, amma duk da haka, hakan na nuna kasar Najeriya na cikin kasashe 40 da suka shara da cin hanci da rashawa.

Ga jerin kasashen nan, inda kasar New Zealand ke kan gaba a karancin cin hanci da rashawa, sai Finland, Sweden da Switzerland. Ita ma kasar Singapore na cikin wadannan kasashe.

Kasashe 10 da suke da karancin cin hanci da rashawa sune:

1. Denmark

2. New Zealand

3. Finland

4. Sweden

5. Switzerland

6. Norway

7. Singapore

8. Netherlands

9. Canada

10. Germany

A dayan hannun kuma, kasashe 10 dake sahun farko wajen cin hanci da rashawa kuma sune:

1. Somalia

2. South Sudan

3. North Korea

4. Syria

5. Yemen

6. Sudan

7. Libya

8. Afghanistan

9. Guinea-Bissau

10. Venezuela

A wani labarin kuma, kungiyoyi masu zaman kansu anan gida Najeriya sun caccaki manufar yaki da cin hanci da rashawa da shugaba Buhari ke yi a gwamnatinsa, musamman yadda ya wanke sakataren gwamnatinsa dangane da zarge zargen satar kudin gwamnati.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Jirgin mata zalla na farko zai sauka Najeriya daga kasar Habasha

Jirgin mata zalla na farko zai sauka Najeriya daga kasar Habasha

Jirgin mata zalla na farko zai sauka Najeriya daga kasar Habasha
NAIJ.com
Mailfire view pixel