Kamfanin Shell ba zata biya diyya ga ‘yan Neja Delta ba - Kotu

Kamfanin Shell ba zata biya diyya ga ‘yan Neja Delta ba - Kotu

- Wata kotun Landan ta hana wasu kauyukan Neja Delta 2 akan neman adalci a kotun shari’a

- An samu zubar man fetur ne a kauyukan sanadiyar sakacin kamfanin Shell

Kamfanin Shell ba zata biya diyya ga ‘yan Neja Delta ba - Kotu

Kamfanin Shell ba zata biya diyya ga ‘yan Neja Delta ba - Kotu

Wata kotun Landan ta yanke hukuncin cewa wasu kauyukan Neja Delta 2 ,wanda kamfanin Shell ta batawa gari sanadiyar zubar mai ba zasu samu diyya ba.

Yankunan biyu sune Ogale da Bille wadanda suka ce shekara da shekarun zubar mai ya gurbata musu ruwan sha su, ya gurbata filin nomansu da kuma kifayen cikin ruwansu.

KU KARANTA: Malamin makaranta ya balla kashin bayan dalibi

BBC AFRICA ta badda rahoton cewa yankunan biyu sun kai karan kamfanin Shell kotu. Karar da sama da masunta 2,000 na garin Bille da kuma wasu 40,000 na garin Ogale a Ogoni suka kai.

Kotun tace karar da aka kawo akan Shell na Najeriya batada alamun samun nasara saboda haka, ba za’a iya cigaba da ita ba.

Kotun tace zubar man a ya faru wanda ya shafi mutane 40,000, kamata yayi akaita kotun da ke zaune a Najeriya ba kasar waje ba.

Lauyoyin yankin Neja Delta sunce zasu daukaka wannan shari’a da akayi.

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Jirgin mata zalla na farko zai sauka Najeriya daga kasar Habasha

Jirgin mata zalla na farko zai sauka Najeriya daga kasar Habasha

Jirgin mata zalla na farko zai sauka Najeriya daga kasar Habasha
NAIJ.com
Mailfire view pixel