Matashi ya sadaukar da rayuwarsa wajen yunkurin hana ‎‘yar kunar bakin wake shiga masallaci

Matashi ya sadaukar da rayuwarsa wajen yunkurin hana ‎‘yar kunar bakin wake shiga masallaci

- Wani dan sakandare, Yakubu Muhammed Fannami, ya rasa rayuwarsa yayin hana wani dan kunar bakin wake shiga cikin masallaci a Maiduguri

- Yakubu Muhammed Fannami dai dan kungiyar kato da gora ne Civilian Joint Task Force (JTF)

- Wasu mambobin Civilian Joint Task Force (JTF) 3 sun jinkita

Matashi ya sadaukar da rayuwarsa wajen yunkurin hana ‎‘yar kunar bakin wake shiga masallaci

Matashi ya sadaukar da rayuwarsa wajen yunkurin hana ‎‘yar kunar bakin wake shiga masallaci

Wani dalibin makarantan Darussalam Science and Islamic Academy (DAISA) ya rasa rayuwarsa yayinda yake kokarin kare rayukan daruruwan mutane a cikin masallacin Kaleri a garin Maiduguri,yayinda wani dan kunar bakin wake ya kai hari anan 25 ga watan Junairu.

KU KARANTA: Adama Barrow zai koma gida

Game da cewar makarantan marigayin a shafinta na Faecbook, yaron ya tare wata yarinya ne yar kunar bakin wake yayinda take kokarin shiga cikin masallaci.

Misalin karfe 5 na safiyar ranan Laraban 25 ga watan Junairu,wasu yan mata masu kunar bakin wake sun kai hari garin Maiduguri kuma wata ta tayar da Bam yayinda aka hanata shiga cikin masallaci lokacin sallan asuba.

Yaron mai suna , Yakubu Muhammad Fannami, mamban kungiyar kato da gora ne wato civilian Joint Task Force (JTF). Ya rasa rayuwarsa a harim. Sauran abokan aikinsa kuma guda 3 an kaisu asibiti.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Farfaɗo da martabar Arewa: Muhimman matakai guda 10 da ya dace yan Arewa su ɗauka – Shehu Sani

Farfaɗo da martabar Arewa: Muhimman matakai guda 10 da ya dace yan Arewa su ɗauka – Shehu Sani

Farfaɗo da martabar Arewa: Muhimman matakai guda 10 da ya dace yan Arewa su ɗauka – Shehu Sani
NAIJ.com
Mailfire view pixel