Babu ruwana da jita-jitan mutuwan Buhari – Bukola Saraki

Babu ruwana da jita-jitan mutuwan Buhari – Bukola Saraki

- Shugaban majalisan dattwan Najeriya yayi kira masu yaa jita-jita cewa su daina hada shi da zancen mutuwan Buhari

- Bukola Saraki yace baiyi niyyan maganan ba amma kiraye-kirayen da ake masa daga gida da waje ya dame sa

- Yace irin wadannan jita-jitan maras asali, na jahilci kuma marasa soyayyan Najeriya ke yada ta

Babu ruwana da jita-jitan mutuwan Buhari – Bukola Saraki

Babu ruwana da jita-jitan mutuwan Buhari – Bukola Saraki

Shugaban majalisar dattawa yayi watsi da maganganun cewa yanada hannu cikin jita-jitan mutuwan Buhari.

Sanatan yace wannan wani dama ne da wasu yan kafafen yada labarai ke son amfani da shi wajen sanyashi cikin jita-jitan mutuwan shugaba Buhari.

Bukola Saraki ya bayyana wannan ne ta mai Magana da yawunsa, Yusuph Olaniyonu,inda yace da farko ma share maganan yayi.

KU KARANTA: Buhari karya yayi - Majalisar dattawa

Yace: “Kiraye-kirayen da akeyi mini daga fadin duniya da gida ne ya wajabta mini inyi Magana akan wannan batu.

“Amma, ya kamata mutane su sani cewa irin wadannan jita-jitan maras asali, na jahilci kuma marasa soyayyan Najeriya ke yada ta

“Irin wadannan maganganu na kawo rashin hadin kai, mumunan zato da rikic ga kasar kuma saboda haka ina baiwa masu kirkira shawaran cewa su daina un yanzu. Bugu da kari, wadannan shegu su daina sanya sunan Sanata Saraki a zancen su.”

Fadar shugaban kasa ta bakin mai shawaran Buhari akan harkokin siyasa, Babafemi Ojudu yace shirme ne yada jita-jitan da akeyi.

"Na karanta wasu labaran ban mamaki cewa wasu gwamnoni na tilasta mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo yayi murabus.

“Kana kuma na amsa wasu waya akan wanna batu. Wannan Magana ba gaskiya bace. Kakale ne kawai.”

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu

Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu

Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu
NAIJ.com
Mailfire view pixel