Sashen wutan lantarki ta kusa tabarbarewa gaba daya – Tony Elumelu

Sashen wutan lantarki ta kusa tabarbarewa gaba daya – Tony Elumelu

- Shugaban Transcorp da bankin United Bank for Africa Tony Elumelu ya bayyana tsoron cewa ba da dadewa ba, bangaren wutan lantarki zata tabarbare

- Elumelu yace Transcorp na bin gwamnati sama da N50 billion saboda rashin aikin kamfanin

- Yace idan ba’a dau mataki ba, bangaren wutan zata tabarbare gaba daya kuma Najeriya zata shiga duhu

Bangaren wutan lantarki ya kusa tabarbarewa gaba daya– Tony Elumelu

Bangaren wutan lantarki ya kusa tabarbarewa gaba daya– Tony Elumelu

Shugaban Transcorp da bankin United Bank for Africa Tony Elumelu ya bayyana tsoron cewa ba da dadewa ba,idan gwamnatin tarayya ba tayi hankali ba bangaren wutan lantarki zata tabarbare gaba daya.

Elumelu ya bayyana cewa Transcorp tana bin gwamnati kudi N50billion kuma idan aka hada da na watan Junairu, zai kai kudi N55billion.

KU KARANTA: An dakatad da karar Murtala Nyako

Vanguard ta bada rahoton cewa ma’aikatar da ke da hakkin tabbatar da cewasashen wutan lantarkin an aiki sosai basu abinda ya kamata.

Elumelu yace: “ Muna bin kudi da yawa. Kamfanin Transcorp Power Holdings na bin N50Billion. idan aka hada da na watan Junairu, zai kai kudi N55billion.

“Shin ta yaya kamfani zata rayu a haka? Wasu kamfunan ma yanzu na san sun fara mutuwa.

“Muna aikine saboda mun fada hanyar neman kudinmu, sauran fa? Wajibi ne ayi dau mataki."

Elumelu ya bayyana cewa lokacin da dalar Amurka ke N168,abubuwa na kyau, amma tun lokacin da ta fara haurawa N300 , abubuwan sun baci.

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Rikici ya barke tsakanin yansanda da sojoji a jihar Ondo

Rikici ya barke tsakanin yansanda da sojoji a jihar Ondo

Rikici ya barke tsakanin yansanda da sojoji a jihar Ondo
NAIJ.com
Mailfire view pixel