Fadar shugaban kasa tayi karya – Majalisar Dattawa

Fadar shugaban kasa tayi karya – Majalisar Dattawa

- Wata takardan da majalisar dattawa ta saki ya nuna cewa Buhari yayi karya akan rahoton Babachir David Lawal

- Shugaban kasan yace mambobin kwamiti 3 ne kacal suka sanya hannu alhalin mutane 6 ne suka sanya

Buhari makaryaci ne – Majalisar Dattawa

Buhari makaryaci ne – Majalisar Dattawa

Domin tsarkake Babachir Lawal, shugaba Muhammadu Buhari yayi ikirarin cewa mambobin kwamitin majalisar dattawa akan binciken tallafi na rikicin arewa maso gabas guda 3 ne kacal suka sanya hannu akan rahoton da ke zargin sakataren gwamnatin tarayya.

Wannan ikirari na shugaban kasa ne yasa akayi watsi da zargin da akeyiwa Mr. Lawal

Shugaban kasa ya bayyana a wata wasikar da ya aikawa shugaban majalisan dattawa Bukola Saraki wanda kuma ya karanta a filin majalisar dattawa na cewa ba zai iya aiki da rahoton da kwamitin ta kawo ba saboda akasarin mambobin kwamitin basu sanya hannu ba kuma ba’a gayyaci Babachir domin yak are kansa.

KU KARANTA: Mutane 10 ke neman tikitin APC

Amma, bayan an gudanar da bincike cikin al’amarin, an gano cewa mutane 6 ne cikin 9 suka sanya hannu cikin takardan.

Shugaban kwamitin, Senator Shehu Sani,yace wannan karya ne, maganan cewa ba’a gayyaceshi ba karya ne zalla.

Game da cewar da jaridar Vanguard, wani kofin rahoton kwamitin ya nuna cewa wasu mambobin kwamitin 4 hade da shugaban kwamitin Shehu Sani, sun rattaba hannu akan rahoton.

Wadanda suka rattaba hannu sune Sanata Ben Murray-Bruce, Tayo Alasoadura, Mallam Ali Wakili, Solomon Adeola, Yahaya Abdullahi, da Isaac M. Alfa.

Mambobin kwamitin 3 ne kacal basu sanya hannu ba. Sune : Sanata T.A. Orji, Oluremi Tinubu, da Mohammed Hassan.

Sanata Shehu Sani yace: “Ina da kofin rahoton wanda mambobi 7 suka rattaba hannu cikin mambobi 9 na kwamitin. Kai koda mutum 3 ne kacal suka sanya hannu ,mun samu hujja”

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili
NAIJ.com
Mailfire view pixel