Buhari bai shirya yakar cin da rashawa ba – PDP ta kai hari ga fadar shugaban kasa

Buhari bai shirya yakar cin da rashawa ba – PDP ta kai hari ga fadar shugaban kasa

- Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) tace Buhari bai shirya yakar cin hanci da rashawa ba

- Jam’iyyar tayi ikirarin cewa wanke Magu da Babachir ya tabbatar da cewa Buhari na son kai

- Sun kira yaki da cin hanci da rashawa da Buhari keyi a matsayin yaudara

Buhari bai shirya yakar cin da rashawa ba – PDP sun kai hari ga fadar shugaban kasa

PDP ta kai hari ga fadar shugaban kasa

Jam’iyyar PDP sun kai hari ga shugaban kasa Buhari kan abunda suka kira yaki da rashawar sa da ta karkata bangare daya.

Jam’iyyar adawan ta maida martani ga wanke shugaban hukumar yaki da cin hanci da yiwa tattalin arziki zagon kasa (EFCC), Mista Ibrahim Magu da babban sakataren gwamnatin tarayya , Mista David Babachir, da yayi daga zargin rashawa.

KU KARANTA KUMA: APC ta sammaci Shehu Sani kan harin baki da ya kaiwa Buhari

A ranar Talata 24 ga watan Janairu kakakin jam’iyyar PDP, Price Dayo Adeyeye yace: “Wanke Magu da Lawal ya tabbatar da hasashen mu na baya cewa ‘yaki da rashawa’ na gwamnatin jam’iyyar All Progressive Congress (APC) yaudara ne; mayar farauta don taozarta mambobin jam’iyyar PDP da kuma makiyan wannan gwamnatin.”

Ya kuma cewa: “Ba sabon labari bane a yanzu cewa an wanke duk wadanda ke aiki a gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ko yan jam’iyyarsa, All Progressive Congress (APC) daga ko wani laifi; duk kuwa da hujoji da za’a kawo.

“Abun damuwa ne ace shugaban kasa ya wanke laifin babban sakataren sa duk kuwa da hujoji masu karfi da majalisar tarayyan Najeriya ke dashi a kan sa, wanda ya nuna cewa Babachir ya karkatar da kwangilar da aka basa na sansanin yan gudun hijira a jihar Borno wanda ya kai sama da naira miliyan 200.

“Haka kuma abun damuwa ne cewa shugaban kasa ya basar da rahoton DSS wanda ya zargi shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu da aikata laifuka daban-dan da rashawa a cikin aikin sa.

Shugaban kasa Buhari bai ga aibu a cikin rahoton ba amma yayi gaggawan gurin ba da umurnin mamaye gidajen alkalai bayan rahoton DSS.

"Haka zalika an wanke shugaban hafsan soji bisa ga dukkan zargin da ake a kansa duk da hujja cewa ya mallaki dukiyoyi a Dubai sama da albashin sa; da kuma hujjar laifukan da ya aikata lokacin da yake aiki a matsayin daraktan makamai a gwamnatin da ta shige.

KU KARANTA KUMA: Trump ya fadi dalilin takaitawa Musulmi shiga Amurka

“Haka kuma, ‘kotun Buhari’ ta wanke ministan cikin gida, Janar Abdulrahman Dambazzau kan mallakar dukiyoyi da ya kai sama da naira biliyan 1.5 a kasar Amurka ; kuma a maimakon a hukunta sa, sai aka bashi kaso mafi girma a kasafin 2017."

A halin yanzu, PDP ta nace kan cewa lallai kasar Amurka ta gayyaci wasu shugabannin duniya kuma cewa an basar da Buhari a bikin nadin Trump.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili
NAIJ.com
Mailfire view pixel