LABARI DA DUMI-DUMI: Gwamnatin tarayya ta karyata taron gwamnoni kan rade-radin mutuwar Buhari

LABARI DA DUMI-DUMI: Gwamnatin tarayya ta karyata taron gwamnoni kan rade-radin mutuwar Buhari

Gwamnatin tarayyan Najeriya ta karyata rahotannin cewa gwamnoni na shirin ganawa a Abuja a yau da kuma tattaunawa a kan lafiyar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

LABARI DA DUMI-DUMI: Gwamnatin tarayya ta karyata taron gwamnoni kan rade-radin mutuwar Buhari

Ministan bayanai Lai Mohammed ya fada wa manema labarai cewa gwamnoni bazasu yi taro ba saboda Buhari na raye

Jaridar Punch ta rawaito cewa gwamnatin tarayya tace rahoton karya ne haka kuma wanda ke cewa gwamnoni na shirin aika wakilai birnin Landan don ganin shugaban kasa.

Ministan bayanai da al’adu Lai Mohammed ne ya bayyana wannan a yayinda ya tarbi mambobin kwamitin shugaban kasa kan Arewa maso Gabas wanda suka kai mai ziyara a Abuja.

KU KARANTA KUMA: APC ta sammaci Shehu Sani kan harin baki da ya kaiwa Buhari

Mohammed ya ce babu bukatar kai ziyarar saboda cewa shugaban kasa na hutun sa ne kawai kamar yadda aka bayyana a wasikar da aka aika majalisa a ranar Al’amis, 19 ga watan Janairu.

A halin yanzu, shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) Sanata Ahmed Makarfi, ya bayyana wadanda ke da alhakin yada jita-jitan mutuwar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ana ta rade-radin cewan shugaban kasa mutu bayan wani rahoton karya da UK Metro tayi na cewa al’amarin ya faru a Jamus ne.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili
NAIJ.com
Mailfire view pixel