APC ta sammaci Shehu Sani kan harin baki da ya kaiwa Buhari

APC ta sammaci Shehu Sani kan harin baki da ya kaiwa Buhari

- Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na fushi da Sanata Shehu Sani

- Sani na wakiltan Kaduna ta tsakiya a majalisa

- Jam’iyyar mai ci na fushi da Sanatan kan furucinsa na kwanan nan game da shugaban kasa Muhammadu Buhari

A jiya 25 ga watan Janairu, Sani dake wakiltan Kaduna ta tsakiya a majalisa ya ga laifin wasikar da shugaban kasa Buhari ya aike wa majalisar dattawa na hukuncin da ya yanke kan babban sakataren gwamnatin tarayya Babachir Lawal.

APC ta sammaci Shehu Sani kan harin baki da ya kaiwa Buhari

Sanata Shehu Sani

A martani ga wasikar wanda shugaban kasa Buhari ya basar da kira ga koran Lawal, Sani yace yayi mamakin cewa za’a iya sa shugaban kasa ya rubuta irin wannan labari.

Ya bayyana wasikar a matsayin “jana’izar yaki da rashawa” a kasar.

KU KARANTA KUMA: Fitacciyar marubuciya Buchi Emecheta ta mutu a Landan

Shugaban jam’iyyar APC na kasa baki daya, Cif John Odigie-Oyegun ya rubuta wata wasika a yammacin jiya wanda za’a aika ga sanatan na gayyatar sa hedkwatan jam’iyyar a Abuja don tattauna sukarsa ga yadda shugaban kasa ya dauki al’amarin zargin rashawa da ake yi a kan Lawal.

Kimanin wata daya da ya wuce, kwamitin kula da wadanda rikin Boko Haram ta cika dasu na majalisar dattawa karkashin jagorancin Sani ta zargi Lawal da aikata zamba na kwangilar sansanin yan gudun hijira a arewa maso gabas.

A wasikar sa ga majalisa, shugaban kasa yayi mamakin yadda akayi majalisar ta yanke shawarar kira ga cire Lawal alhalin ba’a taba kiran babban sakataren na tarayya don kare kansa ba.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili
NAIJ.com
Mailfire view pixel