Musulmai a kasar Amurka sun gudanar da gangamin rashin amince da wani shirin shugaba Donald Trump

Musulmai a kasar Amurka sun gudanar da gangamin rashin amince da wani shirin shugaba Donald Trump

A jiya ne ake sa ran shugaban kasar Amurka Donald Trump zai rattafa hannu kan wasu sabbin dokoki da suka shafi dakatar da duk wani musulmi shiga kasar Amurka da kuma gina katangar karfe a iyakar kasar Amurka da Mexico.

Musulmai a kasar Amurka sun gudanar da gangamin rashin amince da wani shirin shugaba Donald Trump

Shugaba Donald Trump

A cewar hadiman shugaba Trump, sabon shugaban zai fara karyawa ne da dokar gina katangar karfe tsakanin Amurka da Mexico. Kuma shugaban ya tabbatar da wannan zance a shafinsa na Twitter kamar haka:

Musulmai a kasar Amurka sun gudanar da gangamin rashin amince da wani shirin shugaba Donald Trump

Musulmai a kasar Amurka sun gudanar da gangamin rashin amince da wani shirin shugaba Donald Trump

KU KARANTA:‘Ya kamata Inyamuri ya mulki kasar nan a 2019’ – Obasanjo

Gidan talabijin na CNN ta ruwaito a ranar Laraba 25 ga watan Janairu cewar shugaba Trump zai yi tattaki zuwa ofishin jami’an tsaron cikin gida na kasar Amurka don ya basu izinin fara ginin katangar.

Wannan dalili ne ya sanya dubun dubatar musulman kasar yanke shawarar gudanar da zanga zangar nuna rashin amincewa da matakin Trump. Daya daga cikin masu shirya gangamin tace:

Musulmai a kasar Amurka sun gudanar da gangamin rashin amince da wani shirin shugaba Donald Trump

Sanarwar zanga zangar tace: “Mu hadu a dandalin Washington a ranar Laraba da karfe 5 na yamma don gudanar da zanga zanga kin amincewa da matakin da shugaban kasa Trump ya dauka na hana musulmai daga wasu kasashe guda bakwai shigowa kasar Amurka.

“Kasashen kuwa sune Iraq, Iran, Libya, Somalia, Sudan, Syria, da Yemen. Kuma bamu san iya lokacin da za’a dauka ana kaddamar da dokar ba”

Sai dai a wani labarin kuma, shugaba Trump ya cire yaren Spaniyawa daga shafin yanar gizon gwamnatin kasar Amurka, wanda hakan ya baiwa jama’a mamaki matuka.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ku kalli bidiyon da shugaba Trump yayi alwashin dakatar da musulmai daga shiga Amurka.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile faruwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile faruwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile afkuwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma
NAIJ.com
Mailfire view pixel