Halin matsin tattalin arziki: Gwamnatin tarayya zata ƙara ma ma’aikata albashi

Halin matsin tattalin arziki: Gwamnatin tarayya zata ƙara ma ma’aikata albashi

Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yunkura don sake duba yiwuwar kari bisa karancin albashin da ma’aikatanta suke dauka.

Halin matsin tattalin arziki: Gwamnatin tarayya zata ƙara ma ma’aikata albashi

Wannan yunkuri na gwamnatin baya rasa nasaba da kiraye kirayen da kungiyoyin kwadago kamar su NLC da TUC ke yi ma gwamnatin na ganin ta kara yawan karancin albashin ma’aikata daga N18,000 zuwa N90,000, sai dai alamu na nuna cewar gwamnati tafi gamsuwa ta kara albashin zuwa N45,000.

KU KARANTA:Kalli jihohin da zasu amfana daga N375m da shugaba Buhari ya bada na ciyar da yan makaranta

Cikin wata hira da mai baiwa ministan kwadago shawara Nwachukwu Obidiwe yayi da jaridar Punch yace gwamnatin tarayya zata kafa wani kwamiti da zai duba korafin kungiyoyin kwadago dangane da yawan karancin albashi.

Obadiwe ya bayyana cewar za’a kafa kwamitin ne da zarar wata kwamitin da shugaban kasa ya kafa don duba matsalar karancin albashin ta mika rahoton ta a sati mai zuwa, inda daga nan kuma sai a kafa tsayayyen kwamiti mai wakilai daga dukkanin bangarorin da dake da ruwa da tsaki da suka hada da wakilan gwamnatin tarayya, wakilan gwamnatin jihohi da kuma kungiyoyin kwadago.

Obadiwe yace: “Suma kamfanoni masu zaman kansu zasu samu wakilci daga kungiyar tuntuba na masu daukan aiki. Amma dayake watan Janairu yazo karshe, ina sa ran a wata mai zuwa za’a kddamar da wannan kwamiti.”

Tun a shekarar 2016 ne dai gwamnati ta kafa kwamitin mai dauke da mutane 16 wanda aka baiwa aikin samar da hanyoyin rage radadin matsin tattalin arziki a lokacin da gwamnati ta kara farashin mai daga N86 zuwa N145.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016/2017

Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016/2017

Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016/2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel