Rashin shaida ya kawo cikas a shari’ar Nyako

Rashin shaida ya kawo cikas a shari’ar Nyako

– Hukumar EFCC tana zargin tsohon gwamnan jihar Adamawa, Murtala Nyako da yin sama da wasu makudan kudi

– Sai dai rashin shaidu ya hana a cigaba da shari’ar

– Wani Ma’aikacin Banki wanda shine Shaidan EFCC ya tafi hutu daga aiki

Rashin shaida ya kawo cikas a shari’ar Nyako

Rashin shaida ya kawo cikas a shari’ar Nyako

Hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa tana zargin Tsohon Gwamnan Jihar Adamawa watau Murtala Nyako da karkatar da wasu Naira Biliyan 40 a lokacin yana Gwamna. To sai dai yanzu an samu cikas a wajen shari’ar Tsohon Gwamnan.

Rashin samun shaida ne dai ya sa dole aka tsaida shariar. Hukumar EFCC tace shaidan ta, wanda wani Ma’aikacin Bankin Zenith ne ba ya kusa, don kuwa ya tafi hutun aiki. An bayyanawa Kotu cewa shaidan ba zai dawo ba sai tsakiyar Watan Fubrairu.

KU KARANTA: An bude sansanin masu bautar Kasa na Yola

Alkali mai shari’a Okon Abang na babban Kotun Tarayya da ke Abuja yace ba za a cigaba da shari’ar ba saboda karancin hujja. Za dai a cigaba da shari’ar zuwa Ranar 20 ga Watan Fubrairun gobe.

A bara dai Hukumar EFCC ta shiga da Tsohon Gwamna Murtaka Nyako, Kotu gaban Marigayi Alkali Evoh Chukwu. A nan ne Alkali Chukwu ya bada belin tsohon Gwamnan da kuma dan sa na Miliyan 350.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel