Ko da gaske Osinbajo zai sauka daga mukamin sa?

Ko da gaske Osinbajo zai sauka daga mukamin sa?

– Ofishin mataimakin shugaban kasa ya karyata rade-radin cewa ana nema a tursasa Osinbajo yayi murabus

– Mai ba Shugaban Kasa shawara kan harkokin siyasa yayi bayani

– Sanata Ojudu yace wannan karyar banza ce

Ko da gaske Osinbajo zai sauka daga mukamin sa?

Ko da gaske Osinbajo zai sauka daga mukamin sa?

Ana ta yada rade-radin cewa Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo na shirin ajiye aiki bayan matsin lamba da yake samu. Fadar Shugaban Kasa dai ta yi wuf ta maida martani ga masu yada jita-jitar inda tace sam karyar banza ce ba gaskiya ba.

Mai ba Shugaban kasa shawara a game da harkokin siyasa, Sanata Babafemi Ojudu yayi jawabi daga Fadar Shugaban kasar. Sanata Ojudu ya bayyanawa Jaridar Punch cewa rade-radun da ke yawo ba gaskiya bane. Rahotanni sun bayyana a baya cewa wasu Gwamnoni na neman tursasa Osinbajo yayi murabus.

Sanata Ojudu yace babu kanshin gaskiya ko na sisin kwabo a cikin maganar. Yanzu haka dai Mataimakin Shugaban kasar ne ke rike da Kasar a matsayin mukaddashi. Kuma yana kan aiki ba dare ba rana.

KU KARANTA: Gwamnatin Jihar Bauchi tayi kokari

Sanata Shehu Sani mai wakiltar Yankin tsakiyar Kaduna yayi tir tare da mamaki ga martanin wasikar da aka samu daga fadar Shugaban kasa inda aka wanke Sakataren gwamnatin tarayya, Babachir David Lawal daga dukkan zargi.

Sanata Shehu Sani yace Fadar Shugaban Kasa tayi karya a wasikar ta da ta rubutu ga Majalisar Dattawa jiya game da Sakataren Gwamnati. Sanatocin dai sun ce ba za su tabbatar da Magu ba, har sai an tsige Babachir Lawal.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel