Yadda na yi gadi a da domin in samu kudi-Inji wani Minista

Yadda na yi gadi a da domin in samu kudi-Inji wani Minista

– Ministan Ma’adanai, Kayode Fayemi yayi kira ga matasa da su tashi tsaye

– Dr. Fayemi yace har aikin Direba yayi domin ya samu na kashewa…

– Ministan yace yayi aikin gadi a Kasar waje

Yadda na yi gadi a da domin in samu kudi-Inji wani Minista

Yadda na yi gadi a da domin in samu kudi-Inji wani Minista

Ministan Ma’adanai da albarkatun Kasa na Najeriya Dr. Kayode Fayemi yayi kira ga matasan Najeriya, inda ya nemi su da su tashi tsaye haikan wajen neman na su da kuma kawo cigaban al’umma.

Fayemi dai yayi wannan bayani ne kwanaki a Jami’ar Legas inda yace akwai matsalar rashin ba matasa dama a cikin al’umma. Fayemi yace akwai laifin matasan karan kan su don kuwa sun tsaya sake inda bai dace ba.

KU KARANTA: Su wa ke neman ganin bayan Buhari

Fayemi dai ya bayyanawa Daliban Jami’ar cewa su shirya fuskantar rayuwa yayin da suka kammala Jami’a, ko da cewa sun san wasu a Gwamnati. Tsohon Gwamnan na Jihar Ekiti yace yayi aikin gadi da tukin motar haya a Ingila lokacin yana karatu domin ya samu dan sisi.

Kwanaki Sanata Dino Melaye mai wakiltar Yankin Yammacin Kogi yace dole tsofaffin kwanonin nan su tattara ina su-ina su bar shugabancin Kasar. Dino Melaye yace lokaci ne yanzu na matasa masu jini a jika.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim
NAIJ.com
Mailfire view pixel