Abin da tsintsiyar mu ta ke nufi - Bola Tinubu

Abin da tsintsiyar mu ta ke nufi - Bola Tinubu

– Babban jigon Jam’iyyar APC ya bayyana yadda suka kada PDP a zaben baya

– Bola Tinubu yace Mutanen Najeriya sun nemi canji a wancan lokaci

– APC ce ta kare mulkin PDP bayan dogon lokaci

Abin da tsintsiyar mu ta ke nufi-Bola Tinubu

Abin da tsintsiyar mu ta ke nufi-Bola Tinubu

Wani jigo a Jam’iyyar APC mai mulki, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana dabarun siyasar da suka yi har suka naka PDP da Kasa a zaben 2015. Bola Tinubu yayi wannan bayani ne yayin da ya ke gabatar da takarda game da rayuwar siyasar sa a Kwalejin Soji da ke Abuja a Jiya.

Jam’iyyar APC dai ce ta ga karshen PDP bayan ta mulki Kasar na dogon lokaci tun bayan dawowar Damukoradiyya a shekarar 1999. APC ta karbe rinjaye a Majalisar Dattawa da Wakilai na Kasar da ma kuma Jihohi.

KU KARANTA: Anneih yayi tir da masu kiran mutuwar Buhari

Bola Tinubu yace daya daga cikin dabarun da suka yi shine hadaka tsakanin Jam’iyyun adawa a wancan lokaci bayan sun sha kashi a 2011. Tinubu yace daga nan aka nemi take mai ma’ana watau canji da kuma lagon tsintsiya a matsayin wanda za ta share Jam’iyyar PDP. A kamfe dai APC tayi alkawarin abubuwa 3; Tsaro, tattalin arziki da yaki da rashawa.

Kwanakin baya aka yi ta samun bayanai masu nuna cewa Bola Tinubu bai jin dadin abin da yake faruwa a harkar siyasar Kasar. Ake tunanin hakan na iya sa Bola Tinubu da gayyar sa su fice daga Jam’iyyar. Sai dai tuni ya musanya hakan, yace yana nan a APC.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu

Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu

Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu
NAIJ.com
Mailfire view pixel