Tony Anenih yayi Allah wadai da jita-jita game da mutuwar Buhari

Tony Anenih yayi Allah wadai da jita-jita game da mutuwar Buhari

-Tony Anenih yayi Allah wadai da wadanda ke yada jita-jita na mutuwar shugaban kasa Buhari

- Jigon na jam’iyyar PDP yace hakan ya taba faruwa da shi a baya

- Lai Mohammed ya bayyana jita-jitan a matsayin wauta

Tsohon chiyaman na kwamitin amintattu jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) yayi Allah wadai da jita-jitan dake yawo na cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mutu.

Kakakin shugaba Buhari, Garba Shehu ya karyata jita-jitan wanda ya fara yawo bayan shugaban kasa ya kai ziyara birnin Landan.

Tony Anenih yayi Allah wadai da jita-jita game da mutuwar Buhari

Tony Anenih yayi Allah wadai da jita-jita game da mutuwar Buhari

Duk da hakan, wannan bai dakatar da rahotannin cewan lafiyar shugaban kasar na raguwa ba.

Jaridar Cable ta ruwaito cewa Anenih yace shima hakan ya taba faruwa dashi a baya kuma cewa wadanda ke shirya hakan su nemi gafarar Ubangiji.

KU KARANTA KUMA: Magu ne yafi cancanta da matsayin shugaban hukumar EFCC – Buhari

Yace: “Wannan hali na rahotannin karya game da mutuwar shugabanninmu ya zama ruwan dare a kafofin watsa labara kuma ba abune mai kyau ba. Hakan ya taba faruwa dani a shekarar bara lokacin aka ruwaito cewan na mutu a asibitin Landan.

“Hakan ya kuma taba faruwa da tsohon shugaban kasa Ibrahim Babangida a shekarar bara. Ina al’ajabin wadanda ke da alhakin wannan karyan da rahotannin makirci da kuma abunda hakan ke kara masu.

“Yin kasafin mutuwa game da mutun dan uwanka mugunta ne kuma rashin tsoron Allah ne. wannan ya sabawa koyarwar injila cewa muyi wa shugabanninmu da mutane dake jagora addu’a."

Source: Hausa.naija.ng

Related news
In da ranka, ka sha kallo: Yadda wani mutumi ya ƙulla kyakkyawar abota da Zakanya (Hotuna)

In da ranka, ka sha kallo: Yadda wani mutumi ya ƙulla kyakkyawar abota da Zakanya (Hotuna)

Alheri gadon barci: Halayyar kirki da wani mutumi ya nuna ma wata Zakanya ya sa sun shaƙu da juna, kalli hotunan su
NAIJ.com
Mailfire view pixel