Gwamnatin jihar Bauchi ta sada almajirai 176 da yan’uwansu

Gwamnatin jihar Bauchi ta sada almajirai 176 da yan’uwansu

Gwamnatin jihar Bauchi tace ta sada yara almajirai 176 da jami’an tsaro suka kama a Jos da yan’uwansu.

Gwamnatin jihar Bauchi ta sada almajirai 176 da yan’uwansu

Gwamnatin jihar Bauchi ta sada almajirai 176 da yan’uwansu

Zubairu Madaki, kwamishinan matasa da wasanni na jihar Bauchi, ne ya bayyana hakan a Bauchi a ranar Laraba yayinda aka mayar da yaran zuwa jihohinsu da yankunansu.

“A wasu yan kwanakin baya, gwamnatin jihar ta umarcemu da mu ajiye wasu yaran almajirai da aka kama a jihar Plateau amma daga baya an mika su ga masarautar Bauchi.

KU KARANTA KUMA: Mutumin da aka kama a gado da matar dansa yayi ikirarin cewa yayi ne don kudi

“Mu karbe su cikin hali mai kyau muka kuma ajiye su a hedkwatan ma’aikatar kula da jin dadin jama’a tsawon kwanako biyar har sai lokacin da aka gano iyayensu aka kuma kaisu gida.

“Sun kai kimanin 176 daga kananan hukumomi daban-daban na jihar da wasu daga jihohin makwabta,” cewar sa.

Mista Madaki ya bayyana cewa yan karamar hukumar Kirfi dake jihar Bauchi sunfi yawan almajirai 51.

A cewar sa Dambam nada 24, Ganjuwa da Ningi ko wannensu nada 20, Alkeleri 4, yayinda Misau, Bauchi da hukumar Gamawa ke da yara daddaya.

Kwamishinan ya bayyana cewa an mika yaran zuwa ga wakilan kananan hukumominsu ko jihohinsu.

Da yake magana a taron, Mustapha Aliyu, shugaban karamar hukumar Kirfi ya bayyana al’amarin a matsayin abun bakin ciki.

KU KARANTA KUMA: Magu ne yafi cancanta da matsayin shugaban hukumar EFCC – Buhari

Ya bayyana cewa gwamnatin jihar Bauchi ta mika mashi yara 51 da suka fito daga karamar hukumar sa.

Shugaban yace bincike da aka yi ya nuna cewa yaran na hanyarsu ta zuwa makarantar islamiya (almajiranci) kudancin Kaduna lokacin da jami’an tsaron suka kama su a jihar Plateau.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda neman gira na hauren baki a kasar Libya yake janyo musu asarar idanu

Yadda neman gira na hauren baki a kasar Libya yake janyo musu asarar idanu

Yadda neman gira na hauren baki a kasar Libya yake janyo musu asarar idanu
NAIJ.com
Mailfire view pixel