LABARI DA DUMI-DUMI: Ku daure fasto Johnson Suleman cikin kurkuku - MURIC

LABARI DA DUMI-DUMI: Ku daure fasto Johnson Suleman cikin kurkuku - MURIC

Kungiyar MURIC ta umurni jami’an tsaro ta capke fasto Johnson Suleman a kan rikicin kudancin Kaduna.

Fasto Johnson Suleman

Fasto Johnson Suleman

Kungiyar tsare hakkin musulmi, MURIC, ta zargi wani babban fasto cocin Omega Fire Ministries, OFM, fasto Johnson Suleiman. Kungiyar ta ce faston na kokarin haddasa wata fitina ga al’umman Musulmi da kuma Fulani yan bin doka.

A tuna cewa fasto Suleiman ya kasance a cikin labarai kwanan nan bayan ya umurni magoya bayan sa da cewa su kashe duk wani Fulani makiyaya da suka gani a kusa da shi ko kuma cocin sa.

KU KARANTA KUMA: Sojoji zasu mamaye kudancin Kaduna

A wannan safiya, gwamnan Jihar Ekiti Ayodele Fayose ya dakile wani yunkurin DSS na kama babban faston a Ado-Ekiti babban birnin jihar Ekiti.

Amma a cikin wata sanarwar kungiyar daga bakin darekta, Farfesa Ishaq Akintola, kungiyar ta yi Allah wadai da kalaman nuna kyama da banbancin addini da shi fasto Sulieman ke furtawa. Kungiyar MURIC ta kira jami’an tsaro su gaugauta kama fasto Johnson kafin ya haddasa fitina a kasa.

MURIC ta kwatanta kalamai fasto Suleiman a matsayin wata tsokana, rashin hankali da kuma rashin kishin kasa. Kungiyar ta bukaci ‘yan Najeriya da ta nisanci wasu miyagun shugabanin addinai masu adda tanzoma kamar fasto Johnson.

Kungiyar ta kira hukumomin tsaro Najeriya da babban muriya da su yin kokarin magance rikicin tsakani makiyaya da kuma manoman Nijeriya.

Ku kasance tare da mu@ https://www.facebook.com/naijcomhausa

http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Labari mai dadi: Gwamnatin tarayya tayi alkawarin kara albashin ma’aikata a 2018

Labari mai dadi: Gwamnatin tarayya tayi alkawarin kara albashin ma’aikata a 2018

Labari mai dadi: Gwamnatin tarayya tayi alkawarin kara albashin ma’aikata a 2018
NAIJ.com
Mailfire view pixel