"Za’a fara siyar da JAMB" - Inji shugaban Hukumar

"Za’a fara siyar da JAMB" - Inji shugaban Hukumar

Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandari (JAMB) zata fara siyar da takardar nuna sha’awar zana jarabar samun gurbi a makarantun gaba da sakandari na kasar nan (UTME da DE).

"Za’a fara siyar da JAMB" - inji shugaban Hukumar

Farfesa Ishaq Oloyede, shugaban hukumar JAMB

Shuwagabannin hukumar ne suka yanke wannan shawara a yayin wani taro daya gudana tsakanin hukumomin shirya jarabawa daban daban da suka hada da NECO, NABTEB da WAEC a babban ofishin hukumar dake Abuja a ranar Talata 24 ga watan Janairu.

KU KARANTA: Majalisa za ta binciki Jonathan

Hukumomin sun amince da shirya jadawalin zana jarabawar daidai da yadda dalibai masu zana jarabawar, zasu yi hakan cikin kwanciyar hankali.

"Za’a fara siyar da JAMB" - inji shugaban Hukumar

Daraktan watsa labaran hukumar JAMB Dakta Fabian Benjamin ya sanar da haka inda bayyana cewar tsara jadawalin zana jarabawar na bai daya zai taimaka wajen magance matsalolin hadewar jarabwa biyu ko fiye da haka a ranar guda, wanda hakan ke cutar da dalibai.

“hukumonin shirya jarabawa sun yanke shawarar a daga ranar zana jarabawar JAMB don taimaka ma dalibai fuskantar sauran jarabawa kamar su WAEC, NECO da NABTEB.” Inji shi.

A wani labarin kuma, shugaban hukumar JAMB Farfesa Ishaq Oloyede yace za’a sanya kyamara daukan hoto a duk dakunan da za’a zana jarabawar JAMB. Oleyede ya bayyana haka ne yayin dayake jawabi dangane da hanyoyin da suka kamata a bi wajen magance marsalar satar amsa a yayin jarabawa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel