‘Ya kamata Inyamuri ya mulki kasar nan a 2019’ – Obasanjo

‘Ya kamata Inyamuri ya mulki kasar nan a 2019’ – Obasanjo

Tsohon shugaban kasar Najeriya Cif Olusegun Obasanjo ya shawarci al’ummar Najeriya yan kabilar Ibo dasu shiga a fafata dasu a takarar shugaban kasar nan yayin zabukan 2019.

‘Ya kamata Inyamuri ya mulki kasar nan a 2019’ – Obasanjo

Obasanjo ya bayyana haka ne a ranar Talata 24 ga watan Janairu yayin daya karbi bakoncin shugabannin hukumar kiristocin kasar nan (CAN) reshen jihar Ogun a gidansa dake kan tsibirin Abekuta.

Obasanjo yace yana goyon bayan a dawo shugabanci irin na shiyya shiyya, wanda yace hakan zai magance matsalar tsangwama da ake nuna ma wasu bangarori da kabilu, daga nan yace ya kamata a kyale jama’ar Ogun ta yamma ta fitar da gwamnan jihar a zabe mai zuwa.

KU KARANTA: Shin wannan ziyarar Jonathan zai haifar da alheri kuwa?

Obasanjo yace: “Duk da irin tunanin da mutane suke yi ma zaben 2019, ina ganin ya kamata al’ummar kudu maso gabashin kasar nan wato Inyamurai, suma su shiga a fafata dasu a kokarin lashe zaben shugaban kasa.

“Haka nan ma a gida, tun da al’ummar Ijebu da Egba sun samar da gwamna a lokutta daban daban, ya makata yanzu a kyale al’ummar Yewa ko Ogun ta yamma su fitar da gwamna su ma. Idan ba haka ba kuwa zamu waye gari wata rana suna yakan mu da makami saboda rashin adalcin da ake nuna musu. Wannan ra’ayi na ne.”

Kazali Obasanjo yayi tsokaci game da rikicin kudancin Kaduna, inda yace: “Bincike nay a nuna min cewar mutane nata magana ne kan karfi iko kawai, kamata yayi mu fada ma kawunan mu gaskiya, da haka ne kawai zamu magance matsalar.

“Kwatankwacin dukkanin wata matsalar rashin adalci, zaman lafiya ne zai warware su gaba daya, kuma zamu samu zaman lafiya ne kadai idan akwai adalci.”

A wani labarin kuma, rahotanni da NAIJ.com ta samu sun bayyana cewar jigajigan shuwagabannin Arewa sun fara shirin fitar da sabon dan takara da zai kalubalanci shugaba Buhari a zabukan 2019.

Bugu da kari, rahoton namu ya kara fayyace mana Obasanjo na gab da bayyana goyon bayansa ga daya daga cikin tsoffin gwamnonin yankin Arewa Sule Lamido, ko Rabi’u Musa Kwankwaso. Majiyar mu ta shaida mana wannan batu na daga cikin batutuwan da tsohon shugaba Goodluck ya tattauna da Obsanjo yayin daya kai mai ziyara a gidansa a ranar Juma’a 20 ga watan Janairu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel