Za’a fara yi ma Fulani makiyaya rajista a iyakokin kasar nan

Za’a fara yi ma Fulani makiyaya rajista a iyakokin kasar nan

A karshen taron gaggawa da kungiyar gwamnonin jihohin Arewa ta gudanar a jihar Kaduna, kungiyar ta yanke shawarar hada kai da hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki wajen yin rajistan duk bakin hauren makiyaya da zasu shigo kasar nan.

Za’a fara yi ma Fulani makiyaya rajista a iyakokin kasar nan

shugaban kungiyar gwamnonin Arewa Gwamna Kashim Shettima

Shugaban kungiyar gwamnonin Alhaji Kashim Shettima na jihar Barno ya bayyana ma yan jaridu haka a karshen taron nasu a ranar Talata. A cewar gwamnan, sun gano cewar yawancin Fulanin dake da hannu cikin rikicen rikicen da ake yawan samu bay an Najeriya bane, daga kasashen Mali da Sanigal suke shigowa.

KU KARANTA:Sarakuna da gwamnonin Arewa sun tattauna lamarin tsaro a yankin

“Mun samar da sabbin hanyoyin kiwo wanda Fulanin mu na gida zasu dinga amfani dasu ba tare da sun tafi yawon kewaye kasar nan ba.” Inji Shettima.

Bugu da kari shugaba ya jadda bukatar da ke da akwai na duk yan Najeriya dasu hada karfi da karfe wajen samar da tsaro, idan ba haka ba kuwa zamu cigaba da zama koma baya.

Daga karshe ya bayyana shirinsu na ganin duk dan Najeriya yana da daman zama duk inda yake so a kasar nan ba tare da an nuna mai bambamci ba.

Gwamnan yace: “Wasu daga cikin tsofaffin Kano kamar Sabo Bakin Zuwo, da Shekarau duk ba yan asalin jihar bane, daya dan Neja ne, dayan kuma dan jihar Borno ne, amma hakan bai hana su zama gwamnonin jihar ba.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin APC ta saki jerin hanyoyi da gadoji da ta kammala cikin shekaru 2 kacal

Gwamnatin APC ta saki jerin hanyoyi da gadoji da ta kammala cikin shekaru 2 kacal

Gwamnatin APC ta saki jerin hanyoyi da gadoji da ta kammala cikin shekaru 2 kacal
NAIJ.com
Mailfire view pixel