Sanatoci sun bada ka’idoji 3 na tabbatar da Magu

Sanatoci sun bada ka’idoji 3 na tabbatar da Magu

- Sanatoci sun baya da sabbin ka’idojin za’a cika kafin su iya tabbatar da Irahim Magu a matsayin shugaba EFCC

- Wasu sanatoci n suka sanya wannan ka’idoji ,musamman wadanda basu son Magu

Sanatoci sun bada ka’idoji 3 na tabbatar da Magu

Sanatoci sun bada ka’idoji 3 na tabbatar da Magu

Sanatocin da ke da kullaliya da Magu sun bayar da sabbin ka’idojin da za’a cika kafin a iya tabbatar da shi a matsayin shugaban EFCC.

Sanatocin sun bayar da ka’idoji 3 ga shugaba Muhammadu Buhari kafin su iya tabbatar da Ibrahim Magu a matsayin shugaban hukumar hana almundahana da yima tattalin arzikin kasa zagon kasa.

KU KARANTA: An kashe manyan tsagerun Neja Delta

Game da cewar The Nation, daya daga cikin ka’idojin shine shugaba Buhari ya bada takardan dalilin da yasa ya sake dawoda sunan Magu.

Na biyu shine, wajibi ne sai hukumar DSS ta janye rahoton da ta gabatar da majalisar dattawa makonni 6 da suka wuce.

Na uku shine a baida rahoton cewa Magu ya cancanci a tabbatar da shi a gaban kwamitin yaki da rashawa wadanda zasu kuntata shi.

An bayar da waddanan ka’idojin ne a wata ganawar sanatoci a daren Talata,24 ga watan Junairu,domin zama cikas ga Magu.

Yayinda wani sanata yayi Magana akan zancen, yace: “ Inada yakinin cewa tabbatar da Magu ya zama abun Magana a cikinmu, akwai sanatocin da ke so,akwai yan adawan shi.

“A taron sanatoci, mun samu sabani akan shin shugaban majalisar zai karanta wasikar shugaban kasa ko kuma ba zai karanta ba. Bayan da mujadala, shugabancin jam’iyyar sunce a karanta."

https://twitter.com/naijcomhausa

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

Source: Hausa.naija.ng

Related news
‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili
NAIJ.com
Mailfire view pixel