Fayose ya hana DSS damke faston da yace a kashe Fulani

Fayose ya hana DSS damke faston da yace a kashe Fulani

Gwamnan jihar Ekiti kuma shugaban gwamnonin jam’iyyar PDP, Mr Ayodele Fayose, da safiyar yau, Laraba 25 ga watan Junairu, yayi rikici da jami’an hukumar yan sanda liken asiri wato DSS yayainda sukayi yunkurin damke Fasto Johnson Suleiman na cocin Omega Fire a garin Ado-Ekiti.

Fayose ya hana DSS damke faston da yace a kashe Fulani

Fayose ya hana DSS damke faston da yace a kashe Fulani

Faston wanda yazo jihar Ekiti domin wata wa’azin kwanan biyu ya kasance ya fadawa mabiyansa cewa su hallaka duk Fulani makiyayain da suka gani a harabarsa ko na cocinsa a Auchi, jihar Edo. 

Game da rahotannin jaridar Vanguard, An bi Suleiman ne bayan ya kai ziyara ga gwamnan jihar Ekiti a gidan gwamnati zuwa dakin hutunsa da ke unguwan Adebayo.

Sun fasa cikin dakin hutun amma jami’an tsaron gidan suka hanasu. Fasto yayi waya ga Fayose domin fada masa abinda ke faruwa.

KU KARANTA: An bada shawaran sayar da mai N165

Kawai ba da dadewa ba, Fayose da kansa ya jagoranci wata runduna domin hana DSS damke faston mai tayar da kura kuma ya kaishi wani wuri daban.

Johnson yace: “Na amsa waya daga wasu lambobi wadanda ke bukatan sanin inda nike kuma nayi gargadi a masu tsarina cewa kada wani Fulani yazo kusa da ni. Lokacin da jami’an DSS din suka zo ,n azan abinda suka zo yi,sai na kira gwamnan saboda idan suka kama ni, kasar nan zata shiga uku."

Fayose yace: “ NI da kainan na halarci wa’azinsa kuma nayi tunanin ba zai dace ba a kama malamin addini maras rike da makami ba,idan akwai wani abu akanshi,da sun gayyace shi. Naje in kare shi ne. su kashe mu gaba daya."

https://twitter.com/naijcomhausa

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

Kalli bidiyon

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel