Sifeton janar Ibrahim Idris ya kaiwa Buhari ziyara asibitin birnin Landan

Sifeton janar Ibrahim Idris ya kaiwa Buhari ziyara asibitin birnin Landan

- IGP Idris ya jagoranci wata tawaga domin kaiwa Buhari ziyara a birnin Landan

- Wanda tawaga ta kunshi manya a cikin gwamnatin shugaba Buhari

Sifeton janar Ibrahim Idris ya kaiwa Buhari ziyara asibitin birnin Landan

Sifeton janar Ibrahim Idris ya kaiwa Buhari ziyara asibitin birnin Landan

Sifeto janar na hukumar yan sandan Najeiya, Ibrahim Kputom Idris, ya jagoranci wata muhimmin tawaga domin kaiwa shugaba Buhari ziyara asibiti a birnin Landan a ranan Talata, 24 ga watan Junairu yayinda jita-jita ke yaduwa akan lafiyan shugaban kasan.

Wadanda suka takawa Ibrahim Kputom Idris baya sune, DIG na kudi da shugabanci Mr Shuiabu Gambo, kwamishanan aikin dubi, CP Umar Garba da wasu manyan yan sanda.

KU KARANTA:

Game da cewar jaridan Vanguard, yan sandan sun ar babban filin jirgin Nnamdi Azikiwe da ke Abuja ne a da safiyar ranan Talata.

Har yanzu dai ba’a bayyana dalilin wannan tafiya tasu. Tun lokacin da Buhari ya bar Najeriya domin hutu da jinyan kwanaki 10, an samu jita-jitan cewa yayi wafati, amma fadar shugaban kasa ta karyata hakan ta hanyar sakin wata hoton shugaba Buharin yana kallo wata shiri a dakinsa da ke Landan.

https://twitter.com/naijcomhausa

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Rikici ya barke tsakanin yansanda da sojoji a jihar Ondo

Rikici ya barke tsakanin yansanda da sojoji a jihar Ondo

Rikici ya barke tsakanin yansanda da sojoji a jihar Ondo
NAIJ.com
Mailfire view pixel