An kashe wasu manyan Tsagerun Neja-Delta

An kashe wasu manyan Tsagerun Neja-Delta

– An harbe wasu manyan Tsagerun Neja-Delta a Bayelsa

– An dai dade ana neman wadannan Tsageru

– Sai da aka buga tsakanin Jami’an tsaro da Tsaherun

An kashe wasu manyan Tsagerun Neja-Delta

An kashe wasu manyan Tsagerun Neja-Delta

A wani Karen-batta da aka yi tsakanin Jami’an tsaro da Tsagerun Neja Delta, an samu galaba kan tsagerun. Rundunar hadin gwiwar Jihar Bayelsa tayi nasarar harbe wasu biyu daga cikin Tsagerun har lahira.

Tsagerun da aka harbe dai manya ne wadanda aka dade ana cigiyar su. Tsagerun sun addabi Yankin da barna inda suke fasa bututun man Kasar, wanda wannan yake kawo matsalar rashin mai da wuta a fadin Kasar.

KU KARANTA: Sojoji sun gano wata hanyar bakin wake

Laftana Kanal Olaolu Daudu, wanda shine Kwamandan Rundunar Operation Delta Safe ya tabbatar da cewa an harbe wadannan gawurtattun Tsageru da suka gagara. An dai kashe su ne a gwabzawar da aka yi jiya Talata. A ciki akwai wani kasurgumin tsagera da aka sani da Labista.

Kwanan nan Kotu ta yankewa wani Dan Najeriya, Bala Chinda hukuncin daurin rai-da-rai bayan an gano cewa ya kashe wata mata mai zaman kan ta bayan yayi mata fyade. Wannan abu ya faru ne a Kasar Scotland.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Peace Corps ta bukaci babbar kotun tarayya ta gaggauta gabatar da shugaban 'yan sanda gidan kaso

Kungiyar Peace Corps ta bukaci babbar kotun tarayya ta gaggauta gabatar da shugaban 'yan sanda gidan kaso

Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel