Zaben Gwamnan Jihar Anambra: Soludo yaci damara

Zaben Gwamnan Jihar Anambra: Soludo yaci damara

– ‘Yan takara 13 suka fito takarar Gwamnan Jihar Anambra a karkashin Jam’iyyar APC

– Ciki akwai tsohon Gwamnan CBN, Farfesa Charles Soludo

– Jam’iyyar APC tace duk wanda ya iya allon sa ya wanke, ya sha rubutun

Zaben Gwamnan Jihar Anambra: Soludo yaci damara

Zaben Gwamnan Jihar Anambra: Soludo yaci damara

Mutane kusan 13 suke neman tikitin tsayawa takarar kujerar Gwamna a karkashin Jam’iyyar APC a Jihar Anambra a zabe mai zuwa. Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar, Mista Emeka Ibe ya bayyna haka.

A cikin masu neman tsayawa takarar har da tsohon Gwamnan babban Bankin Najeriya na CBN watau Farfesa Charles C. Soludo. Haka kuma rikakken mai kudin nan, Ifeanyi Ubah yana harin kujerar Gwamnan.

KU KARANTA: An bada belin Dasuki tuni Inji Kotu

Sauran masu neman kujerar sun hada da Sanata Andy Ubah da Sanata Uche Ekwunife. Sannan akwai Cif Paul Chukwuma, Cif Obinna Uzor, Tony Nwoye, Prince D. Okonkwo da Cif George Muoghalu. APC dai tace za ta bari duk wanda ya iya allon sa ya wanke.

Gwamnan Jihar Imo, Rochas O. Okorocha yayi kira ga Jama’an sa da su shigo Jam’iyyar APC mai mulki a karshen wannan makon. Gwamna Okorocha yace Mutanen Ibo babu abin da ya dace da su irin su shigo tafiyar APC mai mulkin Kasar. Gwamnan yayi kira ga mutanen sa suyi ta-ka-tsan-tsan lokacin zaben Gwamnan Jihar Anambra mai shirin gabatowa.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC
NAIJ.com
Mailfire view pixel