Tsohon Shugaba Jammeh zai tattara motocin Gwamnati zuwa gida

Tsohon Shugaba Jammeh zai tattara motocin Gwamnati zuwa gida

– Tsohon shugaban kasar Gambia zai tattara ya tafi da motocin da ya saba hawa

– Jammeh zai yi hijira zuwa Kasar Equatorial Guinea

– Sabon Shugaba Adama Barrow ya zabi Fatoumata Tambajang a matsayin ta biyu

Tsohon Shugaba Jammeh zai tattara motocin Gwamnati zuwa gida

Tsohon Shugaba Jammeh zai tattara motocin Gwamnati zuwa gida

Da alamu dai tsohon Shugaban Kasar Gambia, Yahaya Jammeh zai cigaba da rayuwar jin dadi ne ko a zaman gudun hijirar da zai yi. Kwanan nan Adama Barrow ya hau mulkin Kasar bayan Jammeh ya sauka da karfi da jiya.

Yahaya Jammeh zai bar Kasar da motocin Shugaban Kasa wanda ya saba hawa lokacin yana mulki. An dai bar Jammeh ya tafi da ingaramammun motocin har guda 13 zuwa Kasar Equatorial Guinea inda zai yi zaman san a Gudun Hijira.

KU KARANTA: Za a fara koyar da Addinin Kirista a Makarantu

An dai turo motocin cikin jirgin sama inda za a kai wa Tsohon Shugaban. A ciki akwai Motar nan ta Rolls Royce guda 2 da wata Marsandi. Akwai dai motoci 10 da har yanzu ba su shiga cikin jirgi ba tukun kawo yanzu; sun hada da wata zabgegiyar Bentili da kuma Land Roba da wasu Marsandin.

Kwanan nan Sabon Shugaban kasar Gambia, Adama Barrow ya nada Fatoumata Tambajang a matsayin Mataimakiyar sa. Halifa Sallah, mai magana da bakin Barrow ya bayyana haka a wani taro da aka yi jiya da manema labarai a Garin Banjul.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin APC ta saki jerin hanyoyi da gadoji da ta kammala cikin shekaru 2 kacal

Gwamnatin APC ta saki jerin hanyoyi da gadoji da ta kammala cikin shekaru 2 kacal

Gwamnatin APC ta saki jerin hanyoyi da gadoji da ta kammala cikin shekaru 2 kacal
NAIJ.com
Mailfire view pixel