Majalisa za ta binciki Jonathan

Majalisa za ta binciki Jonathan

– Majalisar wakilai ta Tarayya za ta fara binciken kwangilar shigo da risho da aka bada lokacin Shugaba Jonathan

– Honarabul Feleke ya fara tado maganar

– Majalisar za ta duba ta gani ko shin da gaske an yi aikin

Majalisa za ta binciki Jonathan

Majalisa za ta binciki Jonathan

Majalisar wakilai ta Tarayya za ta fara binciken kwangilar da aka bada lokacin Shugaba Jonathan Goodluck na shigo da murafan girki. An dai ware makudan kudi domin shigo da rishon girki, sai dai ana zargi an sace kudin ne kurum.

Jaridar Leadership tace yanzu Majalisa za suyi bincike game da yadda lamarin yake. Shin an kawo rishon da aka fada domin matan kauyukan ko kuwa ya abin yake? An dai ware sama da Naira Biliyan 13 domin sayen rishon girki ga matan karkara.

KU KARANTA: Ka ji abin da Gwamnati za tayi?

Majalisa dai ta nada Kwamitin bincike da na muhalli domin su duba lamarin. Ya kamata dai ace kudi sun rage bayan an sayo risho kusan guda 750,000. Honarabul James Faleke Abiodun ya fara tado maganar, idan ba a manta ba, an bada kwangilar shigo da risho har guda Miliyan 20 lokacin Shugaba Jonathan, sai dai ba a bi ka’ida ba wajen sakin kudin.

Kwanan nan ne Tsohon Gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi ya bayyana cewa ba laifin tsohon shugaba Jonathan Goodluck wajen rashin adana kudin ga Najeriya. Najeriya dai ta samu rarar makudan kudi daga fetur sai dai babu kudin ba labarin su.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel