Shugaba Buhari ya wanke Babachir Lawal

Shugaba Buhari ya wanke Babachir Lawal

– Sanata Shehu Sani yace sam ba Shugaba Buhari ya rubuta wasikar da ta wanke Babachir ba

– A wasikar da aka maido wa Sanatocin martani jiya, shugaban kasa ya wanke Babachir Lawal

– Shehu Sani yace an yi jana’izar yaki da rashawa

Shugaba Buhari ya wanke Babachir Lawal

Shugaba Buhari ya wanke Babachir Lawal

Sanata Shehu Sani mai wakiltar Yankin tsakiyar Kaduna yayi tir tare da mamaki ga martanin wasikar da aka samu daga fadar Shugaban kasa inda aka wanke Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir David Lawal daga dukkan zargi.

Shehu Sani yace Fadar Shugaban Kasa tayi karya a wasikar ta, Sanatan yace ba shakka sun gayyaci Sakataren Gwamnatin domin ya kare kan sa a Majalisar. Haka kuma Sanatan da ya gudanar da bincike game da Sakataren yace kusan ‘yan kwamitin na sa, sun sa hannu a takardar da ya gabatar ba kamar yadda wasikar Shugaban Kasa ta fada ba.

KU KARANTA: An kara shiga Kotu da Dasuki

Shehu Sani dai yayi mamakin yadda Fadar Shugaban Kasa tayi mursisi ta hau kujerar naki game da rokon da aka yi na tsige Sakataren Gwamnati, Babachir David Lawal bisa zargin mikawa Kamfanin sa wasu kwangila.

Shehu Sani yace yanzu an yi jana’izar yaki da cin hanci da rashawa a Gwamnatin Shugaba Buhari. Don kuwa ana tsince wadanda za a bincika ne da laifi a Mulkin na Buhari.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel