Hukumar yaki da fasa-kauri ta gano sabon salon shigo da motoci (HOTUNA)

Hukumar yaki da fasa-kauri ta gano sabon salon shigo da motoci (HOTUNA)

Hukumar yaki da fasa kaurin kayayyaki ta gano wani sabon tsarin fasa kauri da fatake ke amfani da shi wajen shigo da haramtattun kayayyaki.

Hukumar yaki da fasa-kauri ta gano sabon salon shigo da motoci

Reshen hukumar dake kula da jihohin Sakkwato, Kebbe da Zamfara ne ta sanar da haka ta shafin sadarwarta na Facebook inda tace ta gano sabon salon shigo da motoci a cikin manyan motoci inda ake rufe su da itace, ko kuma a cikin kashin shanu don badda kama.

Kaakakin hukumar a reshen jihohin Sakkwato, Kebbi da Zamfara ASCII Musa AY yayi kira ga masu yin wannan fasa kaurin dasu daina, idan ba haka ba kuma zasu saka wando daya dasu.

KU KARANTA:Sarakuna da gwamnonin Arewa sun tattauna lamarin tsaro a yankin

Hukumar yaki da fasa-kauri ta gano sabon salon shigo da motoci

Sanarwar tace:

“Jami’an hukumar kwastam na yankin Sakkwato, Kebbi da Zamfara sun kama wasu motoci da aka yi kokarin yin fasa kaurinsu, inda aka boye su a cikin damin itace. Shugaban reshen hukumar Sani Madugu ya bayyana ma manema labarai cewar an kama motar ne a kan hanyar Tangaza zuwa Ruwawuri.

''Bincike ya nuna ita babbar motar na dauke da wata karamar mota kirar Hinda Accord 2016 mai lamba (IHGCM564867090155). Haka zalika an kama wata Mitsubishi canter mai lamba XA 683 TSF dauke da tarin kashin shanu, sai dai ashe akwai dilan gwanjo 37 daure a ciki.

''Daga karshe shugaban hukumar reshen jihojin Sakkwato, Zamfara da Kebbi yayi kira ga masu aikata fasa kauri dasu daina, idan ba haka ba zasu sanya wando daya dasu.''

Ga wasu daga cikin hotunan:

Hukumar yaki da fasa-kauri ta gano sabon salon shigo da motoci

Hukumar yaki da fasa-kauri ta gano sabon salon shigo da motoci

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda

Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda

Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel