An bayar da belin Dasuki da jumawa - Kotun ta ce

An bayar da belin Dasuki da jumawa - Kotun ta ce

Mai shari’a ta babban kotu babban birnin tarayyan Nijeriya, Abuja Alkali Baba Yusuf ya sake jaddada cewa mai ba tsohon shugaban kasa shawara akan tsaro na kasa, Sambo Dasuki, tuni aka bayar da belin sa.

Dasuki

Makamai

Alkali Baba Yusuf ta babban kotu birnin tarayya, Abuja ya sake jaddada cewa Sambo Dasuki mashawarcin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan akan tsaro na kasa tuni kotu ta bayar da belin sa.

Dasuki ya kasance a tsare fiye da shekara domin zargin yin albazaranci da wasu kudade kimani $2.1 biliyan wanda a ka ware domin siya makamai a karkashin mulkin Jonathan.

Jaridan Daily Trust ta rahoto cewa Alkalin ya ce Sambo Dasuki ya cancanci samu beli ne saboda a baya an bayar da belin sa a shekara 2015 lokacin da gwamnatin tarayya ta gudanar da shi ta hanyar hukumar EFCC da aikata wasu laifuka.

KU KARANTA KUMA: Shin wannan ziyarar Jonathan zai haifar da alheri kuwa?

Hukumar EFCC ta sake gurfanar da Dasuki a ranar Talata, 24 ga watan Janairu da tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa, da wasu mutane hudu da a ke zargi bisa karkatar da wasu kudi kimani N19 biliyan.

Wadanda aka gurfanar da su ne karaman tsohon ministan kudi, Bashir Yuguda, tsohon darektan kudi a ofishin NSA, Shuaibu Salisu, dan Bafarawa, Sagir Attahiru da wata kamfani Bafarawa, Dalhatu Investment Limited.

Mutanen ba su amsa dukan 22 laifi da aka hafka ma su ba.

Kotun ta dakatad da al'amarin zuwa ga watan Fabrairu 24 kafin a fara.

Ku kasance tare da mu@ https://www.facebook.com/naijcomhausa

http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim
NAIJ.com
Mailfire view pixel