Gwamnati ta nemi a fara koyar da ilmin Addinin Kirista a Makarantu

Gwamnati ta nemi a fara koyar da ilmin Addinin Kirista a Makarantu

– Gwamnati ta nemi a fara koyar da Ilmin Addinin Kirista a Makarantun Kasar Swaziland

– Wannan doka za ta fara aiki daga Yau Talata a Kasar

– Gwamnati ta bada umarni a rika karantar da Kiristanci zalla

Gwamnatin Kasar Swaziland ta bada umarnin a rika koyar da Ilmin Addinin Kiristanci a Makarantun fadin Kasar. Wannan doka dai za ta fara aiki ne daga wannan sabon zangon karatun da aka shiga.

Gwamnatin Kasar dai tace Addinin Kiristanci kadai za a koyawa yaran makaranta, tuni ma dai har an kawo kayan aiki. Yanzu haka an fara kawo sababbin litattafan koyon addinin Kiristanci a maimakon wadanda ake da su a da.

KU KARANTA: Dangote da Bill Gates za su yi maganin cutar zazzabi

A wancan makon ne dai Ma’aikatar Ilmi tace a rika koyawa yaran makaranta ilmin Addinin Kirista kadai ba tare da wani Addini ba irin su Musulunci ko Addinin Juda. Wannan dai bakon abu ne a Kasar kwarai da gaske.

An dai kawo wannan doka ne bayan da aka rika samun Musulmai da dama suna shiga cikin Kasar ta Swaziland domin hijira. Shugaban Coci na Kasar ta Swaziland, Stephen Masilela yace Addinin Kiristanci shine babban Addini; wanda ya zama tushe na dukkanin sauran Addinai.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim
NAIJ.com
Mailfire view pixel