Yan sanda sun ci mutuncin dan jarida saboda ya hanasu cin hanci

Yan sanda sun ci mutuncin dan jarida saboda ya hanasu cin hanci

Ana tuhumar wani dan sanda mai suna Akin da laifin cin mutuncin dan jaridan gidan talaijin TVC da direbansa.

Yan sanda sun ci mutuncin dan jarida saboda ya hanasu cin hanci

Yan sanda sun ci mutuncin dan jarida saboda ya hanasu cin hanci

Wani dan jaida mai suna Akiode Temitope,ya garzaya shafinsa na Facebook inda ya bayyana yadda wani dan sanda ya ci masa mutunci tare da direbansa saboda kawai sun ki bayar da cin hanci.

Yace: “ Anyi mini dukan tsaiya,kuma an raunana direba na.”

Akiode yace yana hanyan zuwa Ijebu Ode ne yayinda yan sandan suka tsayar da su domin duba motarsu a Ikorodu. Sunce masa ya basu kudi said an jaridan ya tambaye sa ,shin saboda me?

KU KARANTA: Barrow zai koma Gambiya yau

Karanta bayanin da yayi:

Wannan abu ya faru da ni ne da abokai na a Imota. Mun dau hanyan Ijebu Ode ta hayan Ikorodu sai suka tsayar da mu domin binciken mu, bayan mun nuna musu takardun mota, sai suka bukaci kudi ni kuma nace ta wani dalili zan bashi kudi bayan ya duba takardu na kuma babu matsala, yace inyi masa shiru cewa ni waye da zanyi masa irin wannan Magana, nace masa ni dan jarida ne da kuma abokai na din nan.

''Mun nuna masa ID card din mu. A taikace mun hanasu kudin tare da ogansa mai suna Jude, sai yace zasu tsare mu. Mutanen Imota sukace haka yake tsare mutane akan irin wannan abu. Anyi mini dukan tsiya, kuma an raunana direba na."

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Mata masu juna 100 suka rasa rayukan su a jihar Zamfara - Ma'aikacin asibitin Gusau

Mata masu juna 100 suka rasa rayukan su a jihar Zamfara - Ma'aikacin asibitin Gusau

Mata masu juna 100 suka rasa rayukan su a jihar Zamfara - Ma'aikacin asibitin Gusau
NAIJ.com
Mailfire view pixel