Dangote da Bill Gate zasu hada kai wajen kawo karshen zazzabin cizon sauro

Dangote da Bill Gate zasu hada kai wajen kawo karshen zazzabin cizon sauro

Yaki da zazzabin cizon sauro ya kara samun habbaka yayin da hamshakin attajiri Alhaji Aliko Dangote da shahararren mai kudin duniya lamba daya Bill Gates suka yi alkawarin kawar da cutar ta hanyar hada karfi da karfe da sauran masu ruwa da tsaki.

Dangote da Bill Gate zasu hada kai wajen kawo karshen zazzabin cizon sauro

An shirya wannan aikin hadaka ne a karshen taron tattalin arzikin duniya daya gudana kwanannan a birnin Davos don kawo karshen cutar zazzabin na cizon sauro daga doron kasa.

Shirin kawar da zazzabin sauro na da nufin janyo hankulan mutane ne game da illolin da ciwon ke haifarwa, tare da samar da isassun kudade don tabbatar da an kakkabe ciwon daga cikin al’umma.

KU KARANTA:Ka taɓa ganin hotunan shugaba Buhari masu ban dariya? Duba nan!

Tun a baya, Dangote ya dade yana kira da babban murya da a bada fifiko ga kokarin kawar da cutar zazzabin cizon sauro daga nahiyar Afirka, wanda yace ya hallaka al’ummar nahiyar da dama, musamman matasa da yara kanana. A cewar Dangote, abu ne mai yiwuwa a kawar da cutar daga doron kasa gaba daya.

Wasu daga cikin masu ruwa da tsaki da suka shiga cikin hadakar sun hada da uwargidar gidar Bill Gates, Melinda Gates, Ray Chambers, wakilin sakataren majalisar dinkin duniya na bangaren kiwon lafiya.

ku biyo mu https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Buhari ya amince a sayo jiragen ruwa don toshe kafofin barna da samar da tsaro a hanyoyin ruwa

Buhari ya amince a sayo jiragen ruwa don toshe kafofin barna da samar da tsaro a hanyoyin ruwa

Buhari ya amince a sayo jiragen ruwa don toshe kafofin barna da samar da tsaro a hanyoyin ruwa
NAIJ.com
Mailfire view pixel