LABARI DA DUMI-DUMI: Boko Haram ta kashe sojojin Najeriya biyu

LABARI DA DUMI-DUMI: Boko Haram ta kashe sojojin Najeriya biyu

- 'Yan kuna bakin wake ta hallaka sojojin Najeriya biyu a jiya Talata, 6 ga watan Janairu, 2017.

LABARI DA DUMI-DUMI

Manjo-Janar Lucky Irabor

'Yan kuna bakin wake ta hallaka sojojin Najeriya biyu a jiya Talata, 6 ga watan Janairu, 2017 a inda ita rundinar sojin ta kama biyu daga ‘yan Boko haram.

Babban kwamanda ta operation Lafiya Dole Manjo-Janar Lucky Irabor ya tabattar da rasuwar wadannan sojojin a lokacin da yake ganawa da manema labarai a Maiduguri babban birnin jihar Borno.

KU KARANTA KUMA: Mataimakin gwamnan jihar Delta na rokon yan bindiga su daina kai hare-hare

A cewar Irabor, harin ya faru ne a daren ranar Talata a yankin ta Mate a jihar Borno.

Zai de Janar Irabor bai bayar da sunayen sojojin da suka rasa rayukansu ba.

Rundunar sojin ta kace ‘yan kuna bakin waken da dama, amma abin baƙin cikin shine ta rasa sojoji biyu.

Boko Haram

Kwamanda (Amir) da likita Boko Haram

Sojojin sun gabatar da 'yan ta'adda Boko Haram biyu da suka shiga hanun rundunar sojoji a lokacin gwagwarmayar. Daya daga shugabanin ne kwamandan (Amir) da kuma wani mutum mai matsayin' likita.

KU KARANTA KUMA: Kungiyar CAN ta yabawa Shugaba Buhari

An kama wadannan shugabanin Boko Haram ne a yayin ƙoƙarin samun magani daga garin na jiyya 'yan ta'adda da suka jikkata.

A wata labari rundunar NSCDC ta gafen jihar Borno a ranar da ta gabata Talata, 10 ga watan Janairu, ta ce ta gano wata ma’aunin mai ƙidayar lokaci wanda ‘yan ta’adda Boko Haram ke amfani da ita a lokacin ta da bamai-bamai. Babban kwamandan rundunar, Mallam Ibrahim Abdullahi ya yi wannan furuci a wata ganawa da manema labarai a Maiduguri babban birnin jihar borno.

Ku kasance tare da mu@ https://www.facebook.com/naijcomhausa

http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Aisha Buhari zata karbi baƙoncin Buhari, Osinbajo tare da Ministocin Najeriya a ofishinta

Aisha Buhari zata karbi baƙoncin Buhari, Osinbajo tare da Ministocin Najeriya a ofishinta

Taron Majalisar zartarwa na yau zai gudana a Ofishin Uwargidar shugaban kasa, shin menene dalili?
NAIJ.com
Mailfire view pixel