Jonathan ya musanta zargin cin hancin da akeyi masa

Jonathan ya musanta zargin cin hancin da akeyi masa

Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya musanta zargin da ake yi ma sa na karbar na goro daga kamfanonin mai na Shell da kuma ENI bayan sun samu kwangilar Dala bilyan daya da milyan 300 a shekara ta 2011 a Najeriya.

Jonathan ya musanta zargin cin hancin da akeyi masa

Jonathan ya musanta zargin cin hancin da akeyi masa

Yanzu haka dai wata kotu a birnin Milan na Italiya na gudanar da bincike dangane da wannan zargi, in da aka ce bayan sanya hannu kan wannan kwangila, an bai wa manyan jami’an gwamnatin Najeriya Dala milyan 466, zargin da kakakin Jonathan Ikechukwu Eze ya musanta.

Kazalika zargin ya shafi tsohuwar ministan albarkatun mai na Najeriya, Diezani Alison Madueke.

Sanarwar da kakakin ya fitar ta kara da cewa, babu shakka Mr. Jonathan ya gana da shugabannin manyan kamfanonin mai da ke aiki a Najeriya, in da ya bukace su da su kara kaimi wajen habbaka harkar samar da mai a kasar.

KU KARANTA KUMA: Ma’aikatan Jihar Kwara za su samu sauki

A wani labarin kuma, Shugabannin Kasashen Yammacin Afrika sun soke kai ziyara a wannan Laraba a kasar Gambia a kokarin shawon kan Yahya Jammeh don ganin ya mika ragamar mulki ga Adama Barrow, in da aka dage kai ziyarar har zuwa ranar juma’a mai zuwa.

Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce, duk da cewa an dage ganawar da aka tsara yi a yau laraba, amma fa matsayin shugabannin kasashen yankin na ganin cewa Jammeh ya mika ragamar mulki a karshen wa’adinsa na nan daram.

Wannan kuma na zuwa ne a wani lokaci da babban mai sharia na kasar Emmanuel Fagbenla ya sanar cewa, a cikin watan biyar ko na sha-daya za su saurari batun makudi da Yahya Jammeh ya ce an yi a zaben.

Ku biyo mu a Facebook: https://web.facebook.com/naijcomhausa/

Ku biyo mu a tuwita: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Aisha Buhari zata karbi baƙoncin Buhari, Osinbajo tare da Ministocin Najeriya a ofishinta

Aisha Buhari zata karbi baƙoncin Buhari, Osinbajo tare da Ministocin Najeriya a ofishinta

Taron Majalisar zartarwa na yau zai gudana a Ofishin Uwargidar shugaban kasa, shin menene dalili?
NAIJ.com
Mailfire view pixel