Dalilin da ya hana mu tattaunawa da tsagerun Neja Delta - Buhari

Dalilin da ya hana mu tattaunawa da tsagerun Neja Delta - Buhari

- Tattaunawa tsakanin gwamnatin Najeriya da dattawan yankin Niger Delta ta gagara domin shugaban Najeriya Muhammad Buhari yace ba'a samu dattawa na zahiri ba da zasu tattauna da gwamnati.

- To saidai a wani bangaren wadanda suke kiran kansu dattawan yankin na Niger Delta na cewa hakurinsu ya kusa karewa da gwamnatin Najeriya.

Dalilin da ya hana mu tattaunawa da tsagerun Neja Delta -Buhari

Dalilin da ya hana mu tattaunawa da tsagerun Neja Delta -Buhari

Su kuma 'yan bindigan yankin sun yi ikirarin shirya damarar komawa kai hare-hare kamar na da can kan kamfanonin dake hako man fetur a yankinsu.

Amma bayanai daga fadar shugaban kasa ta bakin mai magana da yawun shugaba Buhari, Malam Garba Shehu yace tattaunawa da dattawan yankin na Niger Delta tana nan.

Yace ba wai an fasa maganar ba ne. Tana nan ana yi amma su dattawan yankin so suke son sai sun zo sun zauna da Shugaba Buhari ida da ido kafin su san da gaske gwamnati ta keyi. Yace akwai manyan jami'an gwamnati irinsu karamin ministan man fetur da shugabannin kamfanoni da na gwamnati a tattaunawar.

KU KARANTA KUMA: Kungiyar CAN ta yabawa Shugaba Buhari

A cewar Garba Shehu, gwamnatin Buhari tana iyakacin kokarinta kuma da yaddar Allah ba za'a ji kunya ba.

Janar Rabe Abubakar mai magana da yawun rundunar tsaron Najeriya ya bayyana irin matakan da suke dauka. Yace hakkinsu ne su kare dukiyoyin Najeriya ko ta halin yaya.

Kwamando Baba Gamawa yace tattaunawa da dattawan yankin ya zama tamkar wasan yara saboda bayan an tattauna da wasu tattawan sai wasu kuma su fito su ce basu yadda ba. Haka ma wata daga yankin tace dattawansu basa magana akan matasan, a'a akan nasu muradun suke tattaunawa.

Ku biyo mu a Facebook: https://web.facebook.com/naijcomhausa/

Ku biyo mu a tuwita: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taron Majalisar zartarwa na yau zai gudana a Ofishin Uwargidar shugaban kasa, shin menene dalili?

Taron Majalisar zartarwa na yau zai gudana a Ofishin Uwargidar shugaban kasa, shin menene dalili?

Taron Majalisar zartarwa na yau zai gudana a Ofishin Uwargidar shugaban kasa, shin menene dalili?
NAIJ.com
Mailfire view pixel